Lauyoyin hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum sun bukaci wata kotun yankin Afirka ta Yamma a ranar Litinin da ta bayar da umarnin a mayar da shi kan mulki, suna masu cewa tsare shi da hambarar da shi da aka yi sun keta haƙƙoƙinsa.
Ana tsare da Bazoum tun bayan da sojoji suka kwace mulki a ranar 26 ga watan Yuli, suna zarginsa da gazawa wajen shawo kan matsalar rashin tsaro a yankin – a ɗaya daga cikin jerin juyin mulki takwas da aka yi a Yammaci da Tsakiyar Afirka a shekaru ukun da suka wuce.
Lauyoyinsa sun shigar da ƙarar a gaban kotun al’umma, wadda aka kafa domin yanke hukunci kan shari’o’inda suka shafi kasashen kungiyar ECOWAS – duk da cewa ba dole ba ne kasashe mambobin kungiyar su bi umurninta, kuma babu wani tsari da zai iya tabbatar da hukuncin nata.
Daya daga cikin lauyoyin tawagar Bazoum, Seydou Diagne ya buƙaci kotun wadda take Abuja babban birnin Nijeriya ta yanke hukuncin cewa "kawo ƙarshe gwamnatin Bazoum da aka yi ta hanya mafi muni tauye haƙƙoƙinsa na siyasa ne".
Diagne, wanda ya yi magana ta saƙon bidiyo daga Dakar babban birnin kasar Senegal, ya ce ya kamata a sako Bazoum ba tare da wani sharaɗi ba, kuma a mayar da shi kan muƙaminsa na shugaban kasa.
Wani labari mai alaƙa
Lauyoyin sun kuma ce tsare shi da ake yi tare da matarsa da ɗansa keta haƙƙoƙinsu na ɗan'adam ne.
Wata lauyan gwamnatin mulkin sojin Nijar, Aissatou Zada ta shaida wa kotun cewa ba a tsare da Bazoum da matarsa da ɗansa ba bisa ka’ida ba.
Ta ce suna da ‘yanci su zo su tafi yadda suka ga dama, amma ana tsare da shugaban ƙasar ne a gida domin tsaron kansa.
Lauyoyin Bazoum sun ce tun ranar 20 ga watan Oktoba ba su samu damar yin magana da shi ba, bayan da gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta zargi tsohon shugaban ƙasar da yunƙurin tserewa tare da taimakon wasu masu abokan hulɗarsa.
Kotun ta sanya ranar 30 ga watan Nuwamba a matsayin wacce za a yanke hukunci kan shari'ar.