Hukumar Hisbah ta Jihar Kano a arewacin Nijeriya ta gargadi masu tuka baburan A-Daidaita-Sahu da su guji duk wata halayya ta rashin da’a da ta saba wa ka’ida da dabi’u da kuma koyarwar addinin Musulunci.
A wani sakon bidiyo da TRT Afrika ta samu daga Hisba, kwamandan hukumar Sheikh Haruna Muhammad Sani ya bayyana wasu halayya hudu da ya ce dole masu sana'ar sufurin ta A-Daidaita-Sahu su guji aikatawa.
Laifukan da kwamandan ya yi gargadi a kan su sun hada da:
- Yin shigar banza
- Lika hotunan tsiraici a jikin ababen hawan
- Kure sautin kade-kade a cikin baburan
- da kuma gwamutsa mutane da yawa da ake yi a lokaci guda musamman ma maza da mata.
"Ya kamata su dinga shiga ta kamala tun da za su dauki mutane ne masu mutunci, sa musu kade-kaden da kuke yi cikin tashin matukar sauti ba daidai ba ne.
"Lika hotuna marasa kyau da kuke da gwamutsa jama'a da yawa a lokaci guda musamman maza da mata duk ba daidai ba ne. Wannan shi ne sakonmu ga 'yan A-Daidaita-Sahu," a cewar Kwamandan Hisbah.
Ya ce jama'ar gari da ke mu'amala da irin wadannan ababen hawa da kansu suka kai korafi ga hukumar Hisba cewa ba sa son hawa duk A-Daidaita-Sahun da suka gani da irin wannan yanayi.
"Duk wanda ya ga irin wannan yanayi ka da ma ya hau wannan A-Daidaita-Sahun. Yaya za ka ga irin haka sannan ka hau? Ai alama za ta nuna maka mai irin wannan halayya to babu tarbiyya a tattare da shi.
Duk mutumin da zai dauki hoton misali ana shan taba ko wasu mugwayen shaidanun aljanu, kuma ka yarda ka hau, to duk abin da ya same ka ai kai ka jawo. Wannan ita ce magana," ya ce.
Sheikh Haruna Sani ya yi kira ga shugabannin kungiyoyin masu jan baburan na A-Daidaita-Sahu da su yi kira ga mutanensu tare da jan kunnuwansu da su daina, musamman ganin tsarin shari'ar Musulunci da ma na hukumomi duk ba sa son hakan.
Ya yi gargadi cewa idan har ba su daina ba to abin da zai biyo baya ba zai yi dadi ba, "amma ba ma so a kai ga hakan," in ji shi.
Sheikh Haruna Sani ya ce wannan doka ba ma 'yan A-Daidaita-Sahu kawai ta shafa ba, ta shafi duk wani mai mu'amala da abin hawa.