Ana yawan samun masu kokarin tsallake Tekun Bahar Rum domin zuwa Turai. / Hoto: Getty Images

Wani kwale-kwale dauke da gomman ‘yan ci-rani ya nutse a gabar tekun Libiya, inda sama da mutum 60 suka rasu, daga ciki har da yara da mata, kamar yadda Hukumar da ke Kula da ‘Yan Ci-rani ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

Hukumar ta bayyana cewa akasarin wadanda ke cikin kwale-kwalen ‘yan Nijeriya ne da Gambiya da sauran kasashen Afirka.

Hatsarin kwale-kwalen shi ne na baya-bayan nan da ya faru a Tekun Bahar Rum, wadda hanya ce mai muhimmanci amma kuma mai muni ga ‘yan ci-rani wadanda ke son samun rayuwa mai inganci a Turai.

Hukumar da ke Kula da ‘Yan Ci-rani ta Majalisar Dinkin Duniya a wata sanarwa ta bayyana cewa kwale-kwalen yana dauke da ‘yan ci-rani 86 a lokacin da igiyar ruwa ta ja shi, lamarin da ja ‘yan ci-rani 61 suka rasu, kamar yadda wadanda suka tsira suka tabbatar.

Hukumar ta bayyana cewa an ceto mutum 25 inda aka kai su wurin tsare ‘yan ci-rani da ke Libiya. Ta bayyana cewa duka wadanda suka tsira na cikin yanayi mai kyau kuma sun samu kulawa mai kyau daga ma’aikata.

Akalla ‘yan ci-rani 940 suka rasu a 2023

Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta bayyana cewa akalla ‘yan ci-rani 940 aka tabbatar sun rasu, 1,248 kuma ba a san inda suke ba tun daga 1 ga watan Janairu zuwa 18 ga watan Nuwamba.

Shirin gano ‘yan ci-ranin da suka yi batan-dabo ya tabbatar da cewa akwai ‘yan ci-rani 14,900 daga ciki har da mata 1,000 da sama da yara 530 wadanda aka kama a lokacin da suke hanyar komawa Libiya a bana.

A 2022, shirin ya gano mutum 529 wadanda suka rasu sannan 848 wadanda suka bace a gabar tekun na Libiya.

Sama da 24,600 aka kama inda aka mayar da su Libiya. Masu safarar mutane a ‘yan kwanakin nan sun rinka amfani da irin rikicin da ake yi a Libiya inda suka rinka fasa-kwabrin mutanen ta iyakokin kasar masu tsawo wadanda suka yi iyaka da kasashe shida.

AFP