Gomman mutane ke mutuwa a Nijeriya duk shekara sakamakon hatsarin kwale-kwale. Hoto/Reuters

Har yanzu masu aikin ceto sun gaza gano ko mutum guda a cikin kusan mutum 200 waɗanda suka yi ɓatan-dabo bayan wani kwale-kwale ya kife da su a Jihar Kogi da ke Nijeriya, kamar yadda wani jami’i a ƙasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Suleiman Makama, wanda shi ne mai magana da yawun Hukumar Kula da Hanyoyin Sufurin Ruwa na Cikin Gida ta Nijeriya ya shaida cewa ma’aikatan da aka aika hanyar ruwa ta Dambo-Ebuchi da ke Kogin Neja wanda a nan ne kwale-kwale ya kife a ranar Juma’a sun gaza gano ko mutum ɗaya a raye ko akasin haka.

“Har yanzu ba mu gano wani daga cikin fasinjoji daga cikin kogin ba. Ana ci gaba da gudanar da aikin ceto,” kamar yadda Makama ya bayyana.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da gudanar da ayyuka nan da kwanaki masu zuwa. Kusan fasinjoji 200 galibi mata ‘yan kasuwa ne da manoma da kuma mazauna yankin da suka shiga kwale-kwale daga jihar ta Kogi da sanyin safiyar Juma’a, suka ɓace bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya kife suna dab da isa wurin da za su sauka.

Ana yawan samun matsalar kifewar kwale-kwale a Nijeriya a duk shekara.

Ko a kwanakin baya sai da masu zuwa taron maulidi fiye da 100 suka rasu bayan kwale-kwalen da suke ciki ya kife da su a hanyar zuwa Jihar Neja.

Ana yawan alaƙanta kifewar kwale-kwale a Nijeriya da yin lodi fiye da ƙima da rashin bin ƙa’idojin da suka dace waɗanda suka shafi sufurin ruwa.

AA