An gudanar da jerin zanga-zanga sakamakon ɗage zaɓen shugaban ƙasar Senegal. / Hoto: AP

Kotun Tsarin Mulkin Senegal ta yi watsi da matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka na ɗage zaɓen da ya kamata a gudanar ranar 25 ga watan nan na Fabrairu.

A hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, kotun ta ce ɗage zaɓen ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar. Ana gani matakin kotun zai jefa ƙasar cikin sabon ruɗani na siyasa

Ƴan takarar jam'iyyun hamayya da ƴan majalisar dokokin da ke ƙarƙashinsu ne suka je gaban kotun a makon jiya inda suka ƙalubalanci wani ƙudurin doka da majalisar dokokin ta amince da shi wanda ya goyi bayan matakin Macky Salla na ɗage zaɓen zuwa watan Disamba.

Matakin ya haddasa zanga-zanga a cikin ƙasar wadda ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum uku sannan yana shan suka daga ƙasashen duniya waɗanda suka ce hakan tamkar yunƙurin juyin mulki ne.

Kotun tsarin mulkin ta ce "ɗage zaɓen ya saɓa wa kundin tsarin mulki," kamar yadda hukunta da aka fitar ya nuna.

Kazalika ta yi umarni ya soke ƙudurin da ya amince a ɗage zaɓen shugaban ƙasar.

Kawo yanzu fadar shugaban ƙasar da kuma gwamnati ba su ce uffan ba game da hukuncin kotun.

Yanzu za a sanya idanu a kan Shugaba Sall, wanda ya ce ya ɗage zaɓen ne sakamakon taƙaddamar da ake yi game da jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa da kuma zargin cin-hanci da ake yi wa Majalisar Tsarin mulki na yin tarnaƙi kan zaɓen ƙasar.

Sai dai ba ta faɗi lokacin da za a gudanar da zaɓen ba, abin da zai bai wa Shugaba Sall sake sanya ranar gudanar da shi ba da daɗewa ba idan ya amince da hukuncin kotun, a cewar Anta Babacar, ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun hamayya, wadda ta yi maraba da hukuncin kotun a matsayin "labari mai faranta rai."

"Babban abin da ƴan takara irina suke jin daɗi game da shi shi ne, daga ranar 2 ga watan Afrilu Macky Sall ba shi ne shugaban ƙasa ba, don haka dole a gudanar da zaɓe tsakanin 25 ga Fabrairu zuwa 2 ga Afrilu," kamar yadda ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho.

Yanzu dai saura kwana 10 kacal kafin ranar da aka tsara gudanar da zaɓen tun da farko kuma galibin ƴan takara ba sa yin yaƙin neman zaɓe tun bayan da Shugaba Sall ya sanar da ɗage zaɓen ana dab da soma kamfe.

TRT Afrika da abokan hulda