Babbar kotun Jamhuriyar Nijar ta cire wa hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum rigar kariya, a wani mataki da ake gani zai bayar da ƙofa a tuhume shi tun bayan kifar da gwamnatinsa.
"An bayar da umarni a cire wa Mohamed Bazoum rigar kariya," a cewar kotun wadda sojoji suka kafa a watan Nuwamba.
Hukumomin sojin Nijar suna zargin Bazoum da cin amanar ƙasa da ɗaukar nauyin 'yan ta'adda da kitsa tuggu ga ƙasar.
Bazoum na tsare a hannun hukumomin sojin Nijar tun da suka yi masa juyin mulki a watan Yulin shekarar 2023.
A watan Agusta, sojojin ƙasar sun sanar da cewa za su tuhume da da laifukan "cin amanar ƙasa da yin ƙafar-ungulu ga tsaron Nijar".
A shekarar 2021 aka zaɓi Bazoum a matsayin shugaban Nijar bayan kammala wa'adin mulkin shekaru takwas na Mahamadou Issoufou, inda ya kasance shugaban farko na farar-hula da ya miƙa mulki ga wani shugaban na farar-hula.
A watan Janairu ne wata kotun soji a Jamhuriyar Nijar ta saki Salem, ɗan Mohamed Bazoum, wanda aka tsare su tare da kuma mai ɗakinsa.