Gwamna Abba K Yusuf

Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin zababben gwamnan jihar Kano.

Kotun ta yanke hukuncin ne ranar Juma'a watanni goma bayan an gudanar da zaben gwamnan na jihar ta Kano mai cike da ce-ce-ku-ce.

Gwamna Abba Gida-Gida ya garzaya Kotun Kolin ne bayan Kotun Daukaka Kara da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe sun ce Nasiru Yusuf Gawuna na APC ne halastaccen gwamnan jihar.

Kotun Kolin ta soke nasarar da kotun sauraren kararrakin zabe da Kotun Daukaka Kara suka bai wa Nasiru Gawuna na APC, tana mai cewa Abba Kabir Yusuf na NNPP ne halastaccen gwamnan jihar.

Jagoran alkalan Kotun, Mai Shari'a John Okoro, ya ce Kotun Daukaka Kara ta yi kuskure da ta tabbatar da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe, wadda ta ce Abba Gida-Gida bai samu kuri'u mafi rinjaye a zaben watan Maris na 2023 ba.

TRT Afrika