Hukuncin Kotun Kolin ta Nijeriya shi ne na karshe don haka 'yan kasar suka zuba ido sosai don ganin yadda za ta kaya.

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta tsaurara matakan tsaro a wasu jihohi da suka hada da Kano da Zamfara da Filato a yayin da Kotun Kolin kasar take shirin yanke hukunci kan zabukan wasu jihohi.

Kotun za ta yanke hukunci ne kan zabukan jihohin Kano da Zamfara da Filato da Legas da Bauchi da Ebonyi da kuma Cross River.

Sai dai shari'a kan zaben jihar Kano ita ce ta fi jan hankalin 'yan kasar.

Gwamnan jihar ta Kano Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ne ya garzaya Kotun Kolin Nijeriya bayan Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da soke zabensa a matsayin gwamna.

Kotun Daukaka Karar ta tabbatar da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe, wadda ta bai wa Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC nasara a zaben da aka gudanar a watan Maris na 2023.

A wancan hukuncin, kotun ta cire kuri'a 165,663 daga kuri'un da Abba Gida-Gida ya samu inda ta ce ba su da inganci, tana mai cewa ba a manna wa kuri'un hatimi ba don haka ba sahihai ba ne.

A jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal Dare ne ya daukaka kara zuwa Kotun Koli inda yake so ta tabbatar da shi a matsayin gwamna, bayan Kotun Daukaka Kara ta soke zaben wasu kananan hukumomi sanna ta bayar da umarni a sake gudanar da zabe.

Kotun ta yi umarni a sake zabe a kananan hukumomin Birnin-Magaji da Bukkuyum da Maradun, abin da gwamnan yake neman kotun ta hana.

A jihar Bauchi, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC Air Marshal Siddique Abubakar ne yake neman Kotun Kolin ta ba shi nasara bayan Kotun Daukaka Kara karkashin jagorancin Mai Shari'a wacce P.T Kwahar, tabbatar da Bala Mohammed Abdulkadir Kaura na PDP a matsayin gwamna.

Labarai masu alaka:

Kotu ta ce ta kori karar ne saboda rashin ƙwaƙƙwaran dalilin da zai sa ta soke zaben, saboda an gudanar da shi bisa turbar da doka ta tanada.

Sai kuma jihar Filato inda Gwamna Caleb Mutfwang na PDP yake neman Kotun Kolin ta sauya hukuncin Daukaka Kara wanda ya ce Nentewe Goshwe na jam'iyyar APC ne halastaccen gwamnan jihar a zaben 2023.

A jihar Legas, dan takarar gwamna a jam'iyyar Labour, Gbadebo Rhodes-vivour da dan takara na jam'iyyar PDP, Abdulazeez Adeniran ne suke neman a soke zaben Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC.

Shi ma dan takarar gwamnan jihar Cross River na jam'iyyar PDP, Sanata Sandy Onor ya garzaya Kotun Kolin inda yake neman ta soke zaben Gwamna Bassey Otu na jam'iyyar APC.

Kazalika Kotun Kolin ta Nijeriya za ta yanke hukunci kan korafin da dan takarar gwamnan Ebonyi a jam'iyyar PDP Chukwuma Odii ya mika mata yana neman ta soke nasarar da Gwamna Fran­cis Nwifuru na jam'iyyar APC ya samu a zaben 2023.

TRT Afrika