Wata kotu a Ghana ta yanke wa mutane shida hukuncin kisa ta hanyar rataya, ciki har da sojoji uku, bisa samunsu da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin kasar shekaru uku da suka gabata.
An kama mutanen ne a shekarar 2021 a lokacin da suke gwajin makamai a wani tsohon wurin harbe-harbe a Accra, babban birnin kasar, bayan wani kutsen leken asiri da aka yi musu ta wayar tarho da ya gano wani shagon kera makamai inda suka ba da umarnin a samar musu makaman, kamar yadda takardun kotu suka nuna.
Dukkan wadanda ake zargi da hannu cikin lamarin sun musanta aikata laifin. An jibge 'yan sanda dauke da manyan makamai a harabar babbar kotun a ranar Laraba a yayin zaman sauraren karar da kuma yanke hukunci.
Daya daga cikin lauyoyin mutane shidan, Victor Adawudu, ya ce tawagar da ke kare wadanda ake zargin za ta garzaya Kotun Kolin kasar domin kalubalantar hukuncin.
An wanke shugaban ‘yan sanda
"Za kuma mu je Kotun Koli domin ta sake duba hujjojin da aka gabatar," in ji shi.
Sai dai babbar kotun ta wanke shugaban ‘yan sanda Benjamin Agordzo da jami’in soji Kanar Samuel Kodzo Gameli da wani karamin soja, Kofur Seidu Abubakar.
''Muna godiya ga Allah, shi kadai ne ya sa hakan ya faru, sun san sharri ne, Ubangijinmu ba ya kuskure. A ko da yaushe ina ji na cikin zuciyata cewar ni 'yantacce ne kuma na san yadda lamarin zai kare," kamar yadda shugaban 'yan sanda Agordzo ya shaida wa manema labarai cikin farin farin ciki bayan da aka wanke shi.
Mutane shidan da suka hada da wani mai kera bindigogi da kuma wani farar-hula ma'aikacin rundunar sojin Ghana, ana tuhumar su da laifin hada baki wajen aikata laifin cin amanar kasa a shekarar 2021.
Sakamakon shari'ar
Babban lauyan kasar Ghana Godfred Yeboah Dame wanda ya jagoranci shari'ar da kara ya yaba da sakamakon hukuncin.
"Wannan hukunci ne mai matukar muhimmanci saboda kundin tsarin mulkin kasar Ghana a matsayin babban dokar kasa, ya bukaci a tabbatar da zaman lafiyar al'ummar kasa, kana ya yi hani sosai kan duk wani yunkuri na hambarar da gwamnati kuma shi ya sa wannan laifi na (cin amanar kasa) hukuncinsa kisa ne," a cewar Dame ga manema labarai bayan shari’ar.
A cewar bayanan kotun, an kama mutanen ne a sansaninsu da ke birnin Accra dauke da makamai da aka kera na cikin gida, da bama-bamai da kuma bindigogin kirar AK-47 da sauran alburusai.
Dame ya ce wadanda ake tuhumar suna cikin wata kungiya ce mai suna Take Action Ghana (TAG) wacce ta shirya gudanar da zanga-zanga, da nufin hambarar da gwamnati.
Tsaurara tsaro
Wannan dai shi ne shari'ar ta farko a Ghana kan cin amanar kasa tun shekarar 1963 lokacin da aka hambarar da gwamnatin shugaban kasar na farko Dr Kwame Nkrumah.
Ghana ta yanke hukuncin kisa ne na karshe a shekara ta 1992 lokacin da ta koma tsarin kundin mulkin kasar.
Wannan sabon hukuncin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Ghana da ke yankin yammacin Afirka, wadda aka santa da kwanciyar hankali a tsarin dimokuradiyya tun 1992, ke fuskantar tsauraran matakan tsaro yayin da yankin ke fama da juyin mulki a 'yan shekarun nan.