Kotun Ghana ta tura 'yar China gidan yari kan hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba

Kotun Ghana ta tura 'yar China gidan yari kan hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba

Tun da farko, Huang ta shaida wa kotun cewa ba ta da laifi, sai dai daga bisani ta amsa laifinta.
Ana yawan zargin 'yan China da ayyukan hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a Ghana. / Hoto: Getty Images

Wata kotu a Ghana ta aika da wata ‘yar China zuwa gidan yari kan samunta da laifin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, kamar yadda lauyoyinta suka tabbatar a ranar Litinin.

An soma shari’ar ne tun a 2017, abin da ya sa aka samu karin haske kan yadda ‘yan China ke da hannu a hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a Ghana.

Kotun wadda ke zama a Accra ta yanke wa Aisha Huang hukuncin zaman kurkuku na shekara hudu da rabi tare da biyan tara ta Cedi 48,000, kimanin dala 4,000 kenan sakamakon hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, kamar yadda lauyanta Hope Agboado ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Tun da farko, Huang ta shaida wa kotun cewa ba ta da laifi, sai dai daga bisani ta amsa laifinta.

Agboado ya bayyana cewa ya roki kotun da ta ci tarar matar sannan ta fitar da ita daga kasar maimakon tura ta gidan yari.

Ya bayyana cewa a halin yanzu shi da Huang suna kokarin yanke shawara kan ko dai su daukaka kara ko kuma kada su yi.

Kasar Ghana mai dumbin arzikin koko da zinare na matukar fuskantar barazana sakamakon hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba inda ake zargin ‘yan China da jagorantar wasu daga cikin ayyukan hakar ma’adinan wadanda suka lalata dazuka da gurbata ruwa.

Hukumar da ke kula da harkokin cocoa a kasar COCOBOD ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a watan Satumba kan cewa Ghana ta yi asarar tan 15,000 na cocoa sakamakon fasa kwabrinsa a gonaki a kakar noma ta 2022/2023.

Reuters