Wata kotu a birnin Landan na Birtaniya ta bayar da umarnin kwace fan miliyan 101.5 (dala miliyan 130.34) daga hannun tsohon gwamnan Jihar Delta ta kudu maso kudancin Nijeriya James Ibori a ranar Juma'a.
A shekarar 2012 wata kotun kasar ta samu Mista Ibori da laifin zamba da halasta kudin haram abin da ya sa aka yanke masa hukuncin zaman kurkuku.
Mai Shari’a David Tomlinson na Kotun Southwark Crown ya ce dole Ibori ya biya kudaden ba tare da bata lokaci ba ko kuma ya fuskanci hukuncin daurin shekara takwas a gidan yari.
Sai dai, Mista Ibori wanda yake Nijeirya a halin yanzu, ya ce zai daukaka kara kan umarnin kwace kudaden.
Tun a lokacin zaman kotun na ranar Alhamis, mai gabatar da kara da wanda ake kara suka gabatar da bukata kan yadda za a lissafa dukiyar da za a kwace bisa dogaro da nazarin da alkalin ya yi.
Jonathan Kinnear, lauyan mai gabatar da kara, ya bayyana wa kotun cewa jimillar kudin da ya kamata a kwace daga hannun Ibori ta kai fam miliyan 101.5, kuma idan ya ki biyan wannan kudi, to ya kamata ya fuskanci karin daurin shekara biyar zuwa 10.
James Ibori, shi ne tsohon Gwamnan jihar Delta daga shekarar 1999 zuwa 2007, kuma yana cikin tsofaffin gwamnonin Nijeriya da suka kai wa Shugaba Bola Tinubu ziyara a fadarsa da ke Abuja a makon jiya.
Tsohon gwamnan ya amsa tuhume-tuhume 10 na zamba da halasta kudin haram da ake masa a shekarar 2012, kuma an yanke masa hukuncin daurin shekara 13 a gidan yari.
An tasa keyarsa daga Dubai zuwa Landan a shekarar 2011 bayan da ya tsere daga Nijeriya.
Mahukunta a Birtaniya sun bayyana shi a matsayin wanda ya sace dukiyar al'umma da halasta kudin haram ta amfani da bankunan Birtaniya da kadarori.
Bayan kwashe shekaru ana shari'a da tsaiko, an kusa kammala kwace kadarorin Mista Ibori.
Alkalin Kotun Southwark David Tomlinson ya yi nazari kan ainihin adadin kudin da Ibori ya ci moriyarsu daga aikata laifukansa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.
An mayar da Ibori Nijeriya a shekarar 2017 bayan ya yi zaman rabin hukuncin da aka yanke masa, ko da yake bai halarci zaman ba.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito shi yana cewa ya shirin daukaka kara dangane da batun umarnin kotu na kwace masa kudi ko dukiya.
Ibori yana cikin manyan 'yan siyasa a Nijeriya duk da samunsa da laifi da kotu ta yi.
Kuma yana da tasiri sosai a jihar Delta, inda yake da hannu wajen samun nasarar duk wani gwamna da ya biyo bayansa ban da Gwamnan jihar mai ci Sheriff Oborevwori.
Birtaniya ta yi alkawarin dawo wa Nijeriya duk wani kudi da aka karbe daga hannun Ibori.
A shekarar 2021, Birtaniya ta mayar wa Nijeriya fam miliyan 4.2 da ta kwace a hannun tsohuwar matar Ibori da 'yar uwarsa, wadanda su ma suka yi zaman kaso saboda taimaka masa da suka yi wajen halasta kudin haram.