Wata Babbar Kotun Tarayya a Nijeriya ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta gurfanar da manyan jami'an gwamnati a jihohin ƙasar bisa laifin tashe-tashen hankula a babban zaɓen 2023.
Kotun, wacce ke zama a birnin Abuja, ta umarci INEC da ta ɗora alhakin laifukan zaɓen 2023, ciki har da rikice-rikice da cin-hanci da sayen ƙuri'u da kuma haɗa-baki a lokacin zaɓen mai cike da ruɗani kan gwamnoni jihohin Nijeriya da mataimakansu da sauransu.
Kazalika kotun ta umurci hukumar da ta gaggauta yin bincike kan tashe-tashen hankula da aka fuskanta a zaɓen 2023 tare da gano waɗanda ake zargi da aikata laifin da masu ɗaukar nauyinsu kana ta tabbatar da an gurfanar da su a gaban ƙuliya.
Umarnin kotun ya biyo bayan ƙarar da wata ƙungiyar farar-hula a Nijeriya wadda ke rajin kare hakkin al'umma da tattalin arzikin ƙasa (SERAP) ta gabatar a gabanta a makon jiya.
''A gaggauta gurfanar da masu laifi a babban zaɓen 2023 a gaban rundunar 'yan sanda da hukumomin yaƙi da cin-hanci da rashawa da manyan laifuka a Nijeria EFCC da ICPC da dai sauransu,'' in ji umarnin da Mai Shari'a Justice Egwuatu ya bai wa kotu.
Mai Shari’a Egwuatu ya ƙara da cewa, “Na yi matuƙar tausayawa tare da tantance bayanan da ke cikin takardar ƙarar da SERAP ta gabatar, kuma ba ni da wani dalilin da zai hana na yarda da bayanan idan aka samu hujjojin da suka tabbatar da bayanan.”
''Wannan muhimmin mataki ne da ke cike da tarihi a Nijeriya a 'yancin 'yan ƙasar na gudanar da sahihin zaɓe da kuma waɗanda rikice-rikicen zaɓuka suka rutsa da su a ƙoƙarinsu na neman adalci da gaskiya wajen yi musu adalci a laifukan da aka aikata a yayin babban zaɓen 2023," in ji mataimakin shugaban ƙungiyar SERAP, Kolawole Oluwadare.