Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya diyyar N30bn ga wadanda aka rushewa shaguna a Filin Idi

Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya diyyar N30bn ga wadanda aka rushewa shaguna a Filin Idi

Kazalika kotun ta hana gwamnatin Jihar Kano shiga cikin filayen da kuma bayar da su ga wani.
Kazalika kotun ta hana gwamnatin Jihar Kano shiga cikin filayen da kuma bayar da su ga wani. Kano Govt

Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano ta umarci gwamnatin jihar da ta biya diyyar naira biliyan 30 ga mutanen da aka rusawa shagunansu a Filin MAsallacin Idi da ke unguwar Ƙofar Mata.

A watan Yunin da ya wuce ne, jim kadan bayan rantsar da sabuwar gwamnatin NNPP karkashin shugabancin Gwamna Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) ta kaddamar da fara rushe wasu wurare a birnin, wadanda ta ce gwamnati da ta gabata ta Abdullahi Umar Ganduje ba ta yi su bisa ƙa’ida ba.

Kwanaki kadan bayan nan ne sai masu shagunan suka kai gwamnatin jihar kara a Babbar kotun Tarayya da ke Kanon, kan rusau din.

A yayin da yake yanke hukuncin biyan diyyar a ranar Juma’a, Mai Shari'ar Samuel Amobeda na Babbar Kotun Tarayyar ta Kano, ya bayyana matakin na rusau a matsayin abin da aka yi ba bisa ka'ida ba.

“Bin dare tare da rushe shagunan talakawa haramtaccen aiki ne mai cike da tsantsar zalunci da ƙeta, don haka lallai gwamnati ta biya masu shagunan, a cewar Mai Shari'a Ameboda, kamar yadda gidan rediyon Freedom ya rawaito.

Kazalika kotun ta hana gwamnatin Jihar Kano shiga cikin filayen da kuma bayar da su ga wani.

Martanin gwamnatin Jihar Kano

A martanin da ta mayar bayan yanke hukunci, gwamnatin Jihar Kano ta bakin Kwamishinanta na Shari'a Barista Haruna Isah Dederi, ta ce za ta daukaka ƙara kan wannan lamari.

A hirar da ya yi da ‘yan jarida Barista Dederi ya ce duk da cewa kowane ɗan ƙasa na da hurumin kai ƙara kotu kan duk abin da bai gamsu da shi ba, amma tun farko masu shigar da ƙarar ba su kai ta kotun da ta dace ba.

“Kar a manta cewa idan mutum ya yi ƙara ya samu umarni daga kotu to ba karshen magana kenan ba. Shari’a ce da tun farko muka shaida wa kotun cewa ba ta da hurumin shigarta, amma tun da ta yi hakan, to tuni dama muka shirya takardun ɗaukaka ƙara a Kotun Daukaka Kara da ke Jihar Kano,” in ji shi.

Barista Dederi ya kuma ce dama ita ma gwamnatin Kano akwai wata karar da ta shigar kan cewa tun asali an ba da wuraren ne ba bisa ƙa’idar shari’a ba, kuma haramun ne.

“Ita Babbar Kotun Tarayya dama ba ta yi shari'a a kan batun waye mamallakin wajen ba, masu ƙarar sun shigar da ƙara ne bisa cewa an rushe musu waje ba bisa ƙa’ida ba, ba bisa da’awar cewa a tabbatar musu da mallakar wajen ba.

“Wannan a yanzu shi ne batun da muka shigar a Babbar Kotun Jiha don ita ce take da hurumi. mun bi ka’idar shari’ar mun daukaka kara kuma mun shigar da sabuwar a babbar kotun jiha.

“Babu yadda za a yi a hana gwamnati yin abin da take ganin shi ne ya dace da al'ummarta. Kowa ya san a tsarin Nijerita dokar mallakar kasa an ɗora ta ne a hannun gwamnan jiha,” Barista Dederi ya faɗa.

TRT Afrika da abokan hulda