Tun 2012 Mali ke fama da rikicin kungiyoyin ta'addanci lamarin da ya kai ga mutuwar dubban mutane./Hoto:AFP

Wata babbar kotu a Mali ta kaddamar da jerin bincike kan ‘yan a-ware na kabilun kasar da kuma kungiyoyin ta’adda da ke da alaka da Al-Qaeda kan ta’addanci da halasta kudin haramun a yayin da rashin tsaro ke ta’azzara a kasar.

Mutanen da ake bincike sun hada da Iyag Ag Ghaly, wani shugaban kabilar Auzunawa kuma jagoran kungiyar Coalition Support Group for Islam and Muslims (GSIM), da kuma fitaccen mai wa’azin nan Bafulatani Amadou Koufa, wanda shi ma dan kungiyar ne, kamar yadda wata takardar umarni daga mai shigar da kara na Kotun Daukaka Kara ta Bamako, wadda aka bai wa kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Talata, ta nuna.

Kazalika akwai shugabanni shida na Auzunawa da ke wata kungiyar kawance ta masu dauke da makamai wadda a kwanakin baya ta yi wa gwamnati tawaye, duk da cewa ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta birnin Algiers a 2015.

Mai shigar da kara ya ce an kaddamar da binciken "ba kawai a kan shugabannin ‘yan ta’adda ba har ma da mambobin kungiyoyin wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a 2015" da kuma wanda "suke da masaniya kan ta’addanci".

Ya bayyana cewa ana zarginsu da "manyan laifuka" wadanda "mai yiwuwa su hada da zargin hada baki don aikata laifuka, da ta’addanci da halasta kudin haramun da daukar nauyin ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba".

Tun shekarar 2012 Mali take fama da masu tayar a kayar baya da ke ikirarin kishin Musulunci wadanda suke kai hare-hare arewacin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.

Daga bisani rikicin ya mamaye kasar har ma ya shiga makwabta irin su Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.

AFP