A watan Maris din 2023 ne hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC ta ayyana Abdullahi Sule a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar. Hoto: Nasarawa Govt

Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta Jihar Nasarawa a arewa maso tsakiyar Nijeriya ta ƙwace nasarar gwamnan jihar Abdullahi Sule na jam’iyyar APC inda ta ayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben 18 ga watan Maris na 2023.

A watan Maris din 2023 ne hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC ta ayyana Abdullahi Sule a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar, a karo na biyu.

Jim kadan bayan hakan ne dan takarar PDP Mista Ombugadu ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar sakamakon.

Gidan rediyon Muryar Nijeriya VON ya ruwaito cewa alkalin da ke jagorantar tawagar alkalan da suka yanke hukuncin, Mai Shari'a Ezekiel Ajayi ya bai wa INEC umarnin cewa lallai ta ƙwace shadiar nasarar cin zaɓen daga hannun Gwamna Sule ta bai wa Ombugadu.

Da yake yanke hukuncin, Mai Shari'a Ezekiel Ajayi ya ce da INEC da Gwamna Sule da Jam'iyyar APC duk sun gaza gabatar da ƙwararan hujjojin kare kansu.

Wannan ita ce shari'a ta biyu da kotunan sauraron karar zabe suka kwace zabe daga hannun gwamnonin da INEC ta ayyana a matsayin wadanda suka yi nasara. A ranar 20 ga watan Satumban da ya gabata ma Kotun zabe ta Jihar Kano ta ƙwace nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf inda ta ce Nasiru Gawuna ne yi nasara a zaben gwamnan jihar.

TRT Afrika