Shugaban Kenya, William Ruto a ranar Juma'a ya zaɓi Ministan Harkokin Cikin Gida Kithure Kindiki a matsayin sabon mataimakinsa bayan tsige Rigathi Gachagua da aka yi.
Shugaban majalisar dokoƙin kasar Moses Wetangula ne ya sanar da zaɓin shugaban ga zauren majalisar, a wani mataki na cike gibin ƙujera na biyu mafi girma a ƙasar.
Wetangula ya shaida wa 'yan majalisar zabin, yana mai share fagen muhawara da kuma kada kuri'a kan tabbatar da naɗin Kindiki a cikin kwanaki masu zuwa.
"A yau da safe, na sami sako daga wurin shugaban ƙasa game da zaɓan Farfesa Kithure Kindiki don cike gurɓin da aka samu a ofishin mataimakin shugaban ƙasar Kenya," in ji Wetangula.
Siyasa ta gaba
A ƙarkashin kunɗin tsarin mulƙin Kenya, dole ne shugaban kasar ya nada wanda zai maye gurbin mukamin mataimakin shugaban kasa a cikin kwanaki 14.
Yayin da Majalisar dokoƙin kasar ita kuma tana da kwanaki 60 domin kada kuri’a kan zaben bayan an kawo gabanta.
A hukumance sanarwar, ta kaddamar da fara aikin tabbatar da mataimakin shugaban ƙasa, inda makomar siyasar kasar ta ta'allaka kan kuri'ar da za a kaɗa.
Nadin Kindiki na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da aka tsige Gachagua daga mukaminsa a kuri’ar da majalisar dattawar ƙasar ta kada mai cike da tarihi, inda aka same shi da laifin cin hanci da rashawa da cin zarafi da kuma nuna kabilanci.
Kindiki ya kasance makusancin Ruto kana ya taba rike mukamin ministan cikin gida kuma ana sa ran zai ba da gudumawa ta ci gaba sosai a gwamnatin bayan hambarar da Gachagua.