Hukumar da ke kula da sararin samaniya ta kasar Kenya ta ce ta jinkirta batun kaddamar da tauraron dan adam dinta na farko zuwa ranar Laraba 12 ga watan Afrilu.
An shirya harba tauraron dan adam na ‘Taifa 1’ wanda yake nufin ‘Kasa Daya’ a harshen Swahili a ranar Talata da misalin 9:40 agogon gabashin Afirka.
Za a harba tauraron ne a cikin kumbon FALCON-9 daga sansanin Vandernberg da ke California a Amurka.
Kamar yadda wata sanarwa da hukumar kula da sararin samaniya ta Kenya ta fitar, kamfanin SpaceX wanda shi ne kamfanin da zai harba tauraron dan adam din, ya bayyana cewa akwai matsaloli na yanayi wadanda za su iya kawo cikas ga kumbon da zai yi jigilar tauraron zuwa sararin samaniya.
Kamfanin na SpaceX yana tsarawa da kerawa da kuma harba kumbo da jiragen sama jannati.
Tauraron dan adam din na Kenya wanda yake dauke da kyamara, zai rinka sa ido kan batun yanayi da ambaliyar ruwa da yanayin tsirrai da kuma illolin sauyin yanayi.
Hukumar da ke kula da sararin samaniya ta Kenya ta bayyana cewa jinkirin da aka samu wurin kaddamar da ‘Taifa 1’ zai shafi wasu kasashen da suke amfani da kumbon da zai yi jigilar tauraron.