Tauraron na Kenya zai taimaka wurin tattara bayanai kan batun noma da kuma hasashen yanayi. Photo/Others

Kenya ta harba tauraron dan adam dinta na farko mai suna Taifa 1.

An daga kaddamar da tauraron dan adam din sau uku saboda rashin ingantaccen na yanayi.

A ranar Juma’a kamfanin SpaceX, kamfanin da ke harba tauraron dan adam, ya dakatar da kaddamarwar dakikoki kafin a harba tauraron.

Sai dai a ranar Asabar, an harba tauraron ta hanyar amfani da wani kumbo mai suna Falcon 9.

Hukumar da ke kula da sararin samaniya ta Kenya ta bayyana cewa tauraron dan adam din zai rinka daukar hotuna domin sa ido kan yanayi da ambaliyar ruwa da noma da albarkatun kasa da sauran illolin sauyin yanayi.

Injinoyin Kenya ne guda tara suka yi aikin samar da tauraron dan adam din inda kasar ta kashe kimanin $370,000.

Sa’o’i kafin Kenya ta harba tauraron nata a ranar Asabar, ita ma Turkiyya ta harba tauraron nata na farko zuwa sararin samaniya mai suna IMECE.

An harba tauraron dan adam din ne da safiyar Asabar daga tashar harba kumbo ta Vandenberg da ke California a Amurka da misalin 06:48 agogon GMT.

Wannan kaddamarwar ta alamta karo na farko da Turkiyya za ta samu tauraron dan adam mai kemara mai karfi a sararin samaniya.

Tauraron dan adam din na Turkiyya zai rinka aiki ne ta bangaren tsaro da kuma sa ido kan bala’o’i da muhalli da ci gaban birni da noma da gandun daji.

TRT Afrika da abokan hulda