Shugabannin sun fadi hakan ne a wajen wani taron manema labarai na hadin gwiwa da aka yi a Kigali/Hoto AA

Shugaban kasar Kenya William Ruto da na Rwanda Paul Kagame sun ce sun yi amannar cewa kungiyar raya kasashen Gabashin Afirka za ta iya warware rikicin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo, DRC.

Shugabannin sun fadi hakan ne a wajen wani taron manema labarai na hadin gwiwa da aka yi a Kigali, babban birnin Rwanda a ranar Talata.

Rikicin na DRC na faruwa ne a tsakanin sojojin Congo da kuma kungiyar ‘yan tawaye mai suna “March 23” da aka fi sani da M23.

A watan Maris din shekarar 2022 ne DRC ta shiga cikin jerin kasashen raya yankin Gabashin Afirka inda ta zama mamba ta bakwai.

A watan Yunin 2022 ne kungiyar EAC ta yarda ta jibge dakarun kasashen yankin a gabashin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo don tabbatar da cewa an tsagaita wuta ba tare da bata lokaci ba.

Kenya ta fara aike nata dakarunta a watan Nuwamban 2022.

Shugaba Ruto ya ce amincewar dakarun kasashen kungiyar EAC ta shiga cikin sabuwar kungiyar raya yankin Gabashin Afirka mataki ne mai kyau.

“A yanzu, Burundi ta aika dakaru don haduwa da na Kenya da suke can tsawon wata shida da suka wuce, Uganda ma ta shgo ciki sannan akwai yiwuwar dakarun Angola ma su shigo don taimakawa wajen daidaituwar al’amura a gabashin DRC,” a cewar Ruto.

Rikicin ya bata alakar diflomasiyya tsakanin DRC da makwabciyarta Rwanda.

A yayin da yake yin jawabi a gaban Baban Taron Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumban 2022, Shugaba Felix Tshisekedi ya zargi Rwanda da goyon bayan kungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke tayar da hankali a Gabashin DRC.

Rwanda wacce ta yi watsi da zarge-zargen tana cewa yana da muhimmanci a fahimci dalilan da suka jawo matsala a Gabashin DRC.

“Ina ga hanya mafi kyau ta magance irin wadannan matsalolin ita ce ta fahimta da kuma magance silar matsalar ko ma duk wata matsala a duk inda take.

“Idan ba a yi duba kan abin da ya jawo matsalolin ba to ba za a iya magance dukkan matsalar ba don haka sai matsalolin su yi ta dawowa a ko yaushe,” in ji Kagame.

Jakadan MDD a DRC ya shaida wa Kwamitin Tsaro na MDD a watan Maris din 2023 cewa yanayin da ake ciki a DRC a watannin baya-bayan nan “ya sake tabarbarewa.”

TRT Afrika