Zancen cancantar Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya ya ci gaba da zama kan kujerarsa bayan ya cika shekara 60 na daɗa jan hankalin jama’a inda 'yan gwagwarmaya ke cewa ya kamata a ce ya yi murabus.
Ranar 31 ga watan Oktoban shekarar 2023 ne dai Kayode Egbetokun ya kama aiki a matsayin sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriya.
Sai dai kuma bayan shekara da kama aikin a matsayin shugaban ‘yan sandan ƙasar ne Kayode ya cika shekara 60 da haihuwa, wato ranar 4 ga watan Satumba.
Wannan ne ya sa ‘yan gwagwarmaya irin su Omoyele Sowore, wanda ya yi takarar shugaban ƙasar Nijeriya a baya, ke ganin ya kamata a ce Kayode ya sauka daga kujerarsa ta shugaban ‘yan sandan ƙasar.
"Ba haka abin yake ba"
Sai dai kuma Antoni Janar kuma Ministan Shari'a na ƙasar, Lateef Fagbemi, da ma rundunar ‘yan sandan ƙasar sun ce lamarain ba haka yake ba.
A wata sanarwar da ya fitar, Fagbemi ya ce an riga an sauya dokar aikin ‘yan sandan Nijeriya ta yadda Sufeto Janar na ‘yan sanda zai kammala wa’adin mulkinsa na shekara huɗu kafin ya yi murabus ko da ma ya cika shekara 60.
“Wannan ya tsawaita wa’adin aikin Egbetokun zuwa ranar 31 ga watan Oktoban shekarar 2027 domin ya cika wa’adinsa na shekara huɗu da aka ba shi,” in ji sanarwar da ministan ya fitar.
“Saboda a kauce wa shakku, ci gaba da zaman Egbetokun a ofis ya dace da dokar aikin ‘yan sandan Nijeriya da aka gyra a shekarar 2024 wadda ta bai wa wanda ke kan kujerar damar ya yi aiki na shekara huɗu daga ranar da aka naɗa shi Sufeto Janar, a nan, daga ranar 31 ga watan Oktobar shekarar 2023,” a cewar Lateef.
Kazalika shi ma mai magana yawun rundunar ‘yan sandan Nijeriya, Olumuyiwa Adejobi ya ambato sashen na 7, sakin layi na 6 cikin dokar aikin ‘yan sandan Nijeriyar wanda ke cewa “wanda aka naɗa a matsayin Sufeto Janar na ‘yan sanda zai kwashe shekara huɗu yana aikin.”
A sanarwar da ya fitar a shafin Facebook na rundunar ‘yan sandan Adejobi ya ce iƙirarin cewa Egbetokun bai dace da ci gaba da kasancewa shugaban ‘yan sandan Nijeriya ba, ba shi da tushe balle makama, yana mai ƙarawa da cewa an yi zargin ne domin yi wa shugabancinsa zagon-ƙasa.