Shugaba Bola Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York na Amurka ba a wannan shekara.
"Don haka shugaban ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Nijeriya," in ji sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasar ta fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Tinubu, wanda ya koma kasar a ranar Lahadin da ta gabata bayan tafiyarsa zuwa kasashen China da Birtaniya, ba zai je Amurkan ba ne saboda yana son mayar da hankali kan al’amuran cikin gida da kuma magance wasu kalubalen da kasar ke fuskanta, musamman bayan da aka yi fama da bala’in ambaliyar ruwa.
A taron Majalisar Dinkin Duniya 79, Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima zai gabatar da jawabin Nijeriya ga babban taron, da halartar muhimman abubuwan da za su gudana a taron, da kuma ganawa da wakilan wasu ƙasashen.
Babban TAron MDD mai taken "Kada a bar kowa a baya: Yin aiki tare don samar da zaman lafiya, dauwamammen ci gaba da mutunta bil'adama a yanzu da a gaba," zai gudana ne daga ranar Talata 24 zuwa ranar Asabar 28 ga watan Satumban 2024.