Wasu kasashen Afirka rainon Faransa sun fara mayar wa Shugaban Faransa Emmanuel Macron martani dangane da kalaman da ya yi cewa shugabannin Afirka sun mance ba su yi wa Faransa godiyar taimaka musu da ta yi ba, lokacin yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a yankin Sahel.
Firaministan Senegal Ousmane Sonko yana daya daga cikin shugabanni daga Yammacin Afirka da ya tanka wa Macron.
Sonko ya ce babban kuskure ne kalaman da Shugaban Faransar ya yi kan Ƙasashen Yammacin Afirka.
Ita ma kasar Chadi ta bayyana damuwarta kan kalaman Macron kuma ta ce kalaman nasa raini ne ga Afirka, kamar yadd Ministan Harkokin Wajen Kasar Abderaman Koulamallah ya bayyana yayin wani jawabi da ya yi a talabijin a ranar Litinin.
Ministan Harkokin Wajen ya ce shi ba shi da matsala da Faransa. Sai dai ya ce akwai bukatar shugabannin Faransa su riƙa daraja Afirka.
Sannan ya ce ai ita ma Faransar mantawa ta yi, don kuwa ba ta yi godiya kan da rawar da kasar Chadi da nahiyar Afirka suka taka wajen ’yanto Faransa yayin yaƙin duniya na daya da kuma na biyu ba.
Kazalika ya ce gudunmawar da Faransa ta bai wa Chadi lokacin da ta kwashe lokaci a cikin kasar ya fi raja’a ne kan muradun Faransar ba tare da yin wani abu da zai kawo ci gaba ga rayuwar mutanen Chadi ba.
Idan za a tuna a karshen watan Nuwamba ne, kasar Chadi ta kawo karshen alaƙar soji da kasancewar sasanin sojin Faransa a cikin kasarta kuma kasar Chadi ta bayyana hakan da “tsohon ya yi.”
Shugaba Macron ya yi kalamansa kan Afirka ne yayin da yake jawabi da manyan ma’aikatan diflomasiyyar kasarsa a ranar Litinin.
Ya ce idan ba domin ɗaukin da Faransa ta kawo yankin Sahel ba, to da yanzu babu sauran wata kasa a yankin da za ta kasance mai ’yancin kanta.
Faransa ta fara dafa wa Mali ne a shekarar 2013 yayin da kasar take kokarin yaki da ’yan aware wanda daga bisani Faransar ta ajiye dakarunta a can da kuma wasu kasashen yankin Sahel.
Sai dai a baya bayan nan kasashen yankin Sahel uku wadanda suke karkashin mulkin soji wato Nijar da Mali da Burkina Faso sun kori sojojin Faransar daga kasashensu.
Kazalika kasashen Senegal da Côte d’Ivoire, wadanda su ba a karkashin mulkin soji suke ba, su ma sun bi sahu wajen umartar sojojin Faransar su fice daga kasashensu.