Gwamnatin kasar Chadi ta bai wa wasu ma'aikatan diflomasiyya hudu na Sudan wa'adin awa 72 su fita daga kasar sakamakon wasu "kalamai masu nauyi" da jami'an Sudan suka yi cewa Chadi na rura wutar rikicin Sudan.
Ma'aikatan diflomasiyyar sun hada da babban jami'in diflomasiyya a ofishin jakadancin Sudan da ke Chadi, da babban jami'in tsaron ofishin da kuma ma'aikata biyu, kamar yadda gwamnatin Chadi ta bayyana ranar Asabar.
An dauki matakin ne bayan wani babban jami'in sojin Sudan Janar Yassir al-Attaya ya yi "kalamai masu nauyi marasa dalili," sannan shi ma ministan harkokin wajen Sudan ya maimaita su a wani gidan talbijin, in ji sanarwar da kakakin gwamnatin Chadi ya fitar.
"Wadannan kalamai da jami'in gwamnatin Sudan suka yi a kan Chadi da gwamnatin kasarmu ba abu ne da za mu amince da shi ba , kuma suna tunzura jama'a sannan cike suke da wata kullalliya," a cewar sanarwar.
Kawo yanzu gwamnatin Sudan ba ta ce uffan game da korar da Chadi, wadda ke makwabtaka da ita, ta yi wa jami'anta ba.
Yaki ya barke a Sudan tun watan Afrilu tsakanin dakarun sojin kasar da na rundunar Rapid Support Forces (RSF) lamarin da ya yi sanadin kisan dubban mutane, sannan miliyoyi suka tsere daga gidajensu, ciki har da dubbai da suka tsallaka cikin Chadi.