Kamfanonin sadarwa a Nijeriya sun buƙaci gwamnatin ƙasar ta amince su yi ƙarin kaso 100 bisa 100 na kuɗin waya ga ‘yan ƙasar.
Idan gwamnati ta amince da wannan ƙarin, hakan na nufin idan ana cajinka naira 10 a duk minti ɗaya idan ka kira waya, zai koma naira 20.
Yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise a Nijeriya, shugaban kamfanin MTN a ƙasar Karl Toriola ya ce tuni suka aika da buƙatar wannan ƙarin ga hukumomin ƙasar.
Mista Karl ya koka kan yadda kamfanonin sadarwa a ƙasar ke gwagwarmaya da ƙoƙarin tsayuwa da ƙafarsu sakamakon yadda farashin komai ya tsefe a ƙasar.
Ya bayar da misalin cewa farashin man fetur ya ƙaru, da dizel, da farashin kuɗin wuta da kuma yadda suka samu ƙaruwa a irin kuɗin da suke kashewa wurin kula da turakun samar da sabis da sauran abubuwan tafiyar da kamfanoninsu.
Ya bayyana cewa a halin yanzu ba wai maganar samun riba suke yi ba, magana ake ta yaya za a yi su ci gaba da tafiyar da kamfanoninsu.
Mista Karl ya ce duk da sun miƙa buƙatarsu ga gwamnatin ƙasar kan batun ƙarin da suke buƙatar su yi, amma babu tabbaci kan za a amince da hakan, amma a cewarsa, suna da yaƙinin gwamnatin ƙasar za ta yi nazari kan lamarin domin yin abin da ya dace.
Sai dai zuwa yanzu hukumar da ke sa ido kan sadarwa a Nijeriya wato NCC ba ta fitar da sanarwa ko kuma ƙarin bayani game da buƙatar ta kamfanonin sadarwan ba.
Waɗannan bayanan na Mista Karl na zuwa ne bayan a farkon makon nan ƙungiyar kamfanonin sadarwa ta Nijeriya ALTON ta ɓara inda ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar daina samun sabis ɗin waya a wasu sassan ƙasar matuƙar ba a yi ƙarin kuɗin waya ba.
Ƙungiyar Alton ta ce idan aka samu tsaiko ta ɓangaren sadarwa a ƙasar, lamarin zai shafi ɓangarori da dama waɗanda suka haɗa da tsaro da kiwon lafiya da ilimi da kasuwanci.