An sanya hannu kan yarjejeniyar bashin ne a hedikwatar bankin da ke birnin Alkahira na kasar Masar a ranar Laraba./Hoto: NNPCL

Kamfanin mai na Nijeriya, NNPC Limited ya sanar da sanya hannu kan yarjejeniyar ciyo bashin gaggawa daga bankin raya kasuwancin shiga da fitar da kayayyaki na Afirka, wato AFREXIM Bank.

Bashin, wanda ya kai dala biliyan uku, za a yi amfani da shi wajen biyan bashin da ake bin kamfanin na NNPC na danyen mai.

An sanya hannu kan yarjejeniyar bashin ne a hedikwatar bankin da ke birnin Alkahira na kasar Masar a ranar Laraba, kamar yadda NNPCL ya wallafa a shafinsa na X wanda a baya ake kira Twitter.

Bankin na AFREXIM zai samar da kudin nan take don bai wa NNPCL dama ya tallafa wa tsarin gwamnatin tarayya kan hada-hadar kudi da haraji, da daidaita darajar Naira.

TRT Afrika