Vincent Aboubakar ya kara kwallo ta uku ana dab da tashi daga wasan./Hoto:Getty

Tawagar kwallon kafar Kamaru ta samu gurbin zuwa gasar Kofin nahiyar Afirka da za a fafata a shekarar 2024 bayan ta doke Burundi da ci 3-0 ranar Talata.

Kungiyoyin biyu sun kwashe minti arba’in da biyar na farko ba tare da an zura kwallo ba a filin wasan Stade Roumde Adjia da ke birnin Garoua.

Tawagar Budundi ta yi ta kokarin doke Indomitable Lions a gidanta, amma fitaccen golansu Andre Onana, ya yi ta buge kwallayen.

Dan wasan Kamaru Bryan Mbeumo ne ya soma zura kwallo bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, yayin Christopher Wooh ya cilla kwallo ta biyu ta ragar Burundi.

Vincent Aboubakar ya kara kwallo ta uku ana dab da tashi daga wasan.

Hakan na nufin Kamaru ce ta daya a rukuni na uku inda ta samu maki bakwai, yayin da Namibia ke biye mata da maki biyar.

Wannan shi ne karo na ashirin da daya da Kamaru za ta je gasar Kofin nahiyar Afirka, wadda ta karbi bakunci a shekarar 2021.

TRT Afrika da abokan hulda