Kamaru ta karbi kashin farko na rigakafin zazzabin cizon sauro, Mosquirix wanda kamfanin sarrafa magunguna na kasar Burtaniya GSK ya samar, yayin da al'ummar kasar ke fama da cutar maleriya da ke kashe mutane sama da 600,000 a duk shekara a duniya.
A ranar Talata da maraice ne aka sauke alluran rigakafin 331,200 - wanda aka fi sani da RTS,S - a filin jirgin sama na Nsimalen na Yaounde, wanda ya sa Kamaru ta zama kasa ta farko a Afirka da ta karbi maganin, bayan shirye-shiryen gwaji a Ghana da Kenya da Malawi.
Zazzabin cizon sauro na daya daga cikin cututtukan da suka fi kashe mutane a nahiyar Afirka, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, inda ta kashe yara ‘yan kasa da shekaru biyar kusan rabin miliyan.
Ministan Lafiya na Kamaru Manaouda Malachie ya bayyana cewa za a fara rarraba alluran rigakafin zuwa gundumomi 42 daga cikin 203 na kasar.
"Mun rasa ’yan uwa da yawa da ke mutuwa saboda wannan cuta. A yau, muna da allurar rigakafin da ta zo don ƙara yawan matakan da aka riga aka fitar," Malachie ya gaya wa manema labarai a Nsimalen.
Za a fara yi wa mutane allaurar rigakafin a watan gobe ko farkon shekara mai zuwa, a cewar wani jami'in kiwon lafiya da ya nemi a sakaya sunansa, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.
GSK ta ce tuni aka yi sama da yara miliyan 1.7 a Ghana da Kenya da Malawi kashi daya na alluran rigakafin, kuma za a yi amfani da ita a wasu kasashe tara masu fama da zazzabin cizon sauro, wadanda Kamaru ke daya daga cikinsu, daga farkon shekara mai zuwa.
Ana sa ran karin allurai miliyan 1.7 na rigakafin RTS,S za su isa kasashen Burkina Faso da Laberiya da Nijar da Saliyo nan da makonni masu zuwa, in ji gamayyar kungiyar samar da rigakafi ta duniya GAVI a wata sanarwar hadin gwiwa da WHO da UNICEF da suka fitar.
Sauran kasashen Afirka za su karbi alluran a cikin 'yan watanni masu zuwa.
Wakiliyar UNICEF Juliette Haenni ta ce lokaci ne mai cike da tarihi don kare yara.
"Mun fi damuwa da yara. Wadanda muke hari su ne 'yan watanni shida zuwa 24 - wadanda suka fi rauni," in ji Haenni.
WHO ta ce allurar rigakafin zazzabin cizon sauro na biyu da Jami’ar Oxford ta Burtaniya, R21/Matrix-M ta samar, za ta fara samuwa nan da tsakiyar shekara ta 2024.