Ana jima ana fama da rikice-rikice a wasu yankuna na kasashen. Hoto/Getty Images

Chadi da Kamaru na aiki a tare domin kara tsaurara matakan tsaro tsakanin kasashen biyu.

Wannan matakin na zuwa ne bayan kusan dubban mutane sun rasa muhallansu a tsakanin yankunan da ke kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labarai na Kamaru ya ruwaito cewa an dauki wannan matakin bayan ministan tsaron Chadi Daoud Yaha Brahim da kuma takwaransa na Kamaru Joseph Beti Asomo sun tattauna a ranar Talata 3 ga watan Oktoba.

“Ziyarar wannan tawaga mai muhimmanci da kuma tattaunawar da ta yi da takwaranta na Kamaru wata hanya ce ta fito da wasu sabbin tsare-tsare na tsaro da kuma dabaru kan yadda za a yaki abokiyar gaba Boko Haram.

"Haka kuma za a dakile wasu nau’ukan hare-hare a kan iyakokinmu kamar ta’addancin kan iyaka da aikata laifuka da rikicin kabilanci,” in ji Beti Asomo.

Asomo ya kara da cewa kare Kamaru da Chadi daga ‘yan tawaye da ‘yan ta’adda zai kasance babbar gudunmawa ga Afirka.

Kasashen dai na neman mafita ne a yakin da suke yi da Boko Haram da safarar makamai da ma’adinai ba bisa ka’ida ba da garkuwa da mutane da satar shanu.

TRT Afrika da abokan hulda