Gwamna Uba Sani ya ce zai ci gaba da gudanar da manyan ayyukan ci-gaba a Kaduna duk da taranaƙin da yake fuskanta./Hoto:Uba Sani/X

Kalaman da gwamnan jihar Kaduna da ke Nijeriya, Malam Uba Sani ya yi cewa ya gaji bashin biliyoyin dala da naira daga gwamnatin tsohon gwamna Nasir El-Rufai sun yi matuƙar tayar da ƙura a fagen siyasar ƙasar.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa ya gaji bashin da ya kai $587m da N85bn da kuma tarin ayyukan da ba a gama ba daga gwamnatin Nasir El-Rufai, amma duk da haka bai karaya ba wurin gudanar da ayyukan ci-gaban jihar Kaduna.

Ya faɗi haka ne a wurin taron da wasu manyan ƴan asalin jihar suka halarta, ciki har da tsohon gwamna Muktar Ramalan Yero da kuma mataimakiyar gwamna Hadiza Balarabe, wadda ita ta yi mataimakiyar gwamna a zamanin mulkin Nasir El-Rufai.

"Duk da bashi mai nauyi na kusan $587m da N85bn da kuma ayyuka ɗari da goma sha biyar da ƴan kwangila ba su gama ba da, abin baƙin-ciki, muka gada daga gwamnatin da ta gabata, mun jajirce wajen ci-gaban Kaduna kuma mun yi bincike mai zurfi lamarin da ya sa muke mayar da hankali kan abubuwan da suka kamata," in ji Gwamna Uba Sani.

Sai dai wannan kalamai ya jawo muhawara sosai musamman a soshiyal midiya kuma nan-take wasu makusanta tsohon gwamna El-Rufai, ciki har da ɗaya daga cikin ƴaƴansa da tsofaffin jami'an gwamnatinsa suka riƙa mayar da martani.

Bashir El-Rufai, ɗa ga tsohon gwamnan na Kaduna, ya ce gwamna Uba Sani na cikin sanatocin da suka amince Nasir El-Rufai ya ciyo bashi a lokacin yana ɗan majalisar dattawa.

Kazalika ya yi wa gwamna Uba Sani shaguɓe cewa "wannan gwamnatin ta Kaduna tana gina ɗakin taro a kan kuɗin da suka kai naira biliyan bakwai amma tana ƙorafi kan bashin da tsohuwar gwamnati ta bar mata."

Sai dai wani mai sharhi a shafin X, Kawu Garba yana ganin cewa Gwamna Uba Sani bai yi kalaman "domin ya ci mutuncin kowa ba" don kuwa ba jihar Kaduna ce kaɗai take cikin ƙangin bashi ba.

Shi kuwa Sanata Shehu Sani, ɗan majalisar dattawa daga jihar Kaduna da ya soki shirin tsohon gwamna El-Rufai na karɓo bashi, ya ce yanzu gaskiya ta yi halinta.

"Allanmu mai girma ya fito da gaskiyata game da batun karɓar basuka a Kaduna," in ji shi.

TRT Afrika