Mataimakin shugaban Nijeriya Sanata Kashim Shettima ya bukaci mutane su guji wallafa sakon taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa a jaridu.
Ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ranar Alhamis.
An haifi Sanata Shettima ranar 2 ga watan Satumba na shekarar 1966 don haka ranar Asabar yake cika shekara 57 a duniya.
Bisa al’ada dai, ‘yan Nijeriya da sauran mutane kamun-kafa kan biya miliyoyin kudi ga jaridu don wallafa sakonnin taya murna ga shugabanni a irin wadannan lokuta.
Sai dai Sanata Shettima ya “ina matukar godiya bisa sakonnin taya murna da mutane da dama daga cikinku” suka aiko a irin wannan rana a shekarun da suka wuce.
Amma a wannan karon, mataimakin shugaban kasar ya ce “Ina kira a gare ku da ku guji wallafa sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwata a jaridu” saboda mawuyacin halin da ake ciki a Nijeriya.
Ya yi kira ga masu son yi masa murna da su yi amfani da kudin wajen bayar da gudunmawa ga kungiyoyin bayar da agaji don su taimaka wa jama’a.