Ɗaya daga cikin manyan ta’addancin da Sharmen ya aikata akwai batun sace ɗaliban Bethel Baptist High School da ke Kujama a ranar 5 ga Yulin 2021. / Hoto: Others

An kashe gawurtaccen ɗan bindigar nan Kachalla Tukur Sharme da wasu muƙarrabansa a yayin wata arangama tsakanin ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a Kaduna.

Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin.

Ma’aikatar ta bayyana cewa baya ga Sharme, akwai wasu ‘yan ta’adda biyu waɗanda ke wata ƙungiya ta ta’addanci ta daban da aka kashe, wanda hakan ya bai wa wasu waɗanda aka yi garkuwa da su damar tserewa.

Sanarwar ta bayyana cewa an kashe Kachalla Sharme a ƙauyen Hambakko da ke yankin Rijana da dajin Kaso, wanda ya ratsa ta cikin Kachia da Chikun da Kajuru.

Bayanan sirri sun tabbatar da cewa akwai ‘yan ta’adda biyar waɗanda suka tsira da raunuka inda a halin yanzu suna gararamba cikin daji suna neman yadda za a yi musu maganin raunin da suka samu.

Sharme, wanda gawurtaccen ɗan ta’adda ne, ya yanka mutane da dama, ya yi garkuwa da ɗaruruwa tare da sace shanu bila’adadin.

Ɗaya daga cikin manyan ta’addancin da Sharmen ya aikata akwai batun sace ɗaliban Bethel Baptist High School da ke Kujama a ranar 5 ga Yulin 2021.

A lokacin har sai da jami’an tsaro biyu suka rasa rayukansu a ƙoƙarin daƙile sace ɗaliban makarantar.

Hakazalika Sharme da muƙarrabansa akasari su ke kai hari Millenium City da Maraban Rido da Kujama da Kajuru da Maro da Kateri da wasu sassa na Kagarko da Kachia da Birnin Gwari duka a Jihar Kaduna.

Haka kuma Sharmen kan kai hare-hare a ƙauyukan Katsina da Neja.

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin arewacin Nijeriya da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, da masu garkuwa da mutane.

A baya-bayan nan jami’an tsaron ƙasar na cewa suna samun nasarar kashe ‘yan ta’addan da suka addabi yankin.

A kwanakin baya ne sojojin ƙasar suka sanar da kashe Halilu Sububu, wanda jagora ne na ‘yan bindiga a arewacin Nijeriya.

TRT Afrika