Ka da a tsawwala farashin kayan abinci yayin Ramadan – Janar Tiani

Ka da a tsawwala farashin kayan abinci yayin Ramadan – Janar Tiani

A wannan makon ne ake sa ran Musulmai a fadin duniya za su fara azumin watan Ramadan na bana.
Abdourahamane Tiani

Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya buƙaci jami’an gwamnatinsa da su dage wajen wayar da kan manyan ’yan kasuwa kan su guji tsawwala farashin kayan abinci kuma su duƙufa wajen tabbatar da wadatuwarsu a lokacin watan azumin Ramadan.

Janar Tiani ya bayyana hakan ne yayin wani zama na musamman kan shirye-shiryen watan Ramadan da ya yi da majalisar ministocinsa a ƙarshen mako.

A wannan makon ne ake sa ran Musulmai a faɗin duniya za su fara azumin watan Ramadan na bana.

Wannan kira da Janar Tiani ya yi yana zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin tabbatar da cewa mutane masu ƙaramin ƙarfi suna samun muhimman abubuwan da suke buƙata ba tare da fuskantar wahala ba, a cewar majalisar ministocin gwamnatin sojin ƙasar.

Kazalika majalisar ministocin gwamnatin sojin ƙasar ta buƙaci dukannin masu ruwa da tsaki ciki har da manyan ’yan kasuwa da ƙungiyoyin fararen-hula da sauran al’umma da su kasance masu taimako da haƙuri da juna. Kuma majalisar ta buƙaci shugabannin addini da su ja hankalin al’umma kan muhimmancin haɗin kan ƙasa da kuma zaman tare.

Ita ma gwamnatin a nata ɓangaren ta jaddada cewa za ta tabbatar da wadatuwar kayayyakin buƙatar yau da kullum a duka faɗin ƙasar.

Sakamakon haka ne ya sa gwamnatin ta fara ɗaukar mataki inda aka tura dakarun ƙasar iyakar ƙasar da Burkina Faso inda suke raka dubban manyan motoci da suke ɗauke da abinci zuwa cikin ƙasar, a cewar majalisar wannan mataki ya taimaka wajen wadatuwar abincin da ake matuƙar buƙata a lokacin watan Ramadan.

Sannan majalisar ta jinjina kan wani mataki da ƙasar ta ɗauka na dakatar da fitar da wasu muhimman kayan abinci daga cikin ƙasar zuwa ƙasashe maƙwabta.

TRT Afrika