Ministan harkokin wajen Aljeriya Ahmed Attaf ya soma rangadi zuwa kasashe uku a Yammacin Afirka domin tattaunawa bayan da aka yi wa makwabciyarta Nijar juyin mulki.
Kwace iko da sojojin na Nijar suka yi a ranar 26 ga watan Yuli ya kada hantar makwabtan Nijar da kuma fadin Yammacin Afirka a daidai lokacin da rikicin masu tayar da kayar baya suka kashe dubban mutane.
Ministan na Aljeriya daga ranar Laraba zai kai ziyara Nijeriya da Jamhuriyyar Benin da Ghana domin tattaunawa da takwarorinsa kamar yadda wata sanarwa daga ma’aikatar ta bayyana.
“Wannan tattaunawar za ta fi mayar da hankali kan rikicin da ake yi a Nijar da kuma hanyoyin da za a shawo kansa,” in ji sanarwar.
Kungiyar ECOWAS ta yi barazanar amfani da karfin soji kan masu juyin mulkin a Nijar domin mayar da Shugaba Bazoum a kan mulki, sai dai kungiyar ta bayyana cewa matakin shi ne na karshe da za ta iya dauka idan duka hanyoyin diflomasiyya sun ki bullewa.
Aljeriya ta yi watsi da duk wani mataki da za a yi amfani da shi kan wannan rikicin inda a farkon makon nan ta hana jiragen Faransa bi ta sararin samaniyarta domin gudanar da ayyuka a Nijar.
A halin yanzu, Aljeriya ba ta tattauna da shugabannin sojojin Nijar ba, haka kuma ba su dauki wasu matakai na rufe iyakokinsu ba.