Amurka ta ce ta daina bayar da tallafi ga Gabon sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi ranar 30 ga watan Agustan da ya gabata.
Wata sanarwa da kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar Matthew Miller ya fitar ranar Litinin ta ce "za mu ci gaba da bayar da tallafi ne idan muka ga gwamnatin rikon kwarya ta dauki kwararan matakai na komwa kan turbar mulkin dimokuradiyya."
Amurka, wadda da ma ta dakatar da bai wa kasar wasu tallafi, ta kara da cewa a hukumance yanzu ta tabbatar an yi juyin mulki a Gabon abin da ke nufin ba za a ci gaba da bai wa kasar taimakon jinkai ba kamar yadda dokokin Amurka suka tanada.
Sojojin Gabon sun kifar da gwamnatin dadadden shugaban kasa Ali Bongo Ondimba a daidai lokacin da hukumar zaben kasar ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara karo na uku a zaben da aka gudanar wanda ke cike da zargin tafka magudi.
An ayyana Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban rikon kwarya yayin da aka nada Raymond Ndong Sima, fitaccen mai adawa da Bongo, a matsayin firaiminista.
Ndong Sim ya roki kasashen Yamma kada su kwatanta juyin mulkin da aka yi a Gabon da wadanda aka yi a wasu kasashen Afirka, yana mai cewa sojoji sun kifar da gwamnatin kasar ne domin hana tarzoma da shawo kan matsalar cin-hanci da rashawa.
Tuni dai aka daure Sylvia Bongo Ondimba Valentin, matar tsohon shugaban kasar, kan zarge-zargen almubazzaranci da kudaden al'umma.