Faransa ta ce shirin ficewar sojinta daga Chadi “ya danganta ne game da daidaitawa da mahukuntan Chadi.” Hoto : AFP

Faransa ta janye jiragen yaƙinta daga Chadi bayan rashin jituwa tsakaninta da hukumomi a Chadi, kamar yadda wata sanarwa daga Ma’akatar Tsaron Faransa ta bayyana.

“Tare da la’akari da wannan matakin... rundunar sojin Faransa a yau ta janye kayan yaƙinta da ke cikin N’Djamena,” a cewar ma'aikatar a ranar Talata.

“Kasancewar waɗannan jiragen na biyan buƙatar da abokan hulɗarmu suke so ne,” in ji ta.

Ta ce shirin ficewar sauran madafun ikon sojin Faransa daga Chadi “ya danganta ne ga yadda suka yi da mahukuntan Chadi.”

Kasawar Faransa

Ma’aitakar Harkokin Wajen Chadi ta bayyana ƙarshen hulɗar soji da Faransa ranar 28 ga watan Nuwamba, in ji ma’aikatar tsaron Faransa a wata sanarwa.

Ce-ce-ku-ce ya kaure tsakanin ƙasashen biyu saboda rashin jituwa na ɓangaren tsaro da diflomasiyya, in ji kafafen watsa labaran Faransa.

Majiyoyi daga Chadi sun ce sojojin Faransa sun ƙi ba da tallafi na sama da kuma bayanan sirri ga mahukuntan Chadi a watan Oktoba, a lokacin da suke fuskantar farmaƙi daga ‘yan ta’addan Boko Haram, in ji kafafen watsa labaran Faransa.

Kalaman Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Noel Barrot a lokacin da ya ziyarci Chadi a ƙarshen watan Nuwamba sun ƙara taƙaicin, in ji rahotanni.

Rahotannin sun ce Barrot ya ba da shawarar a ɗage zaɓen da za a yi a watan Disamba.

Mai masauƙin ƙarshe

Chadi ta kafa wani kwamiti na musamman a makon jiya domin sake duba yarjejeniyoyin da ta rattaba hannu kansu tare da Faransa, kuma masu zanga-zanga sun yi jerin gwano a babban birnin ƙasar N’Djamena domin nuna goyon baya ga matakin.

Chadi ta kasance ƙasa ta ƙarshe da ke da sojin Faransa a yankin Sahel bayan da Paris ta janye sojojinta daga Mali da Burkina Faso da kuma Nijar.

Dangantakar Faransa da Mali da Burkina Faso ta taɓarɓare bayan sojoji sun yi juyin mulki a ƙasashen a shekarun 2020 da 2022.

Mutane a Mali da Burkina Faso, ƙasashe biyu da Faransa ta yi wa mulkin mallaka, sun yi zanga-zangar ƙin amincewa da zaman Faransa a ƙasashensu.

TRT Afrika