Jiragen sojin Nijeriya sun yi luguden wuta kan 'yan ta'adda da suka buya a karkashin bishiyoyi a Borno

Jiragen sojin Nijeriya sun yi luguden wuta kan 'yan ta'adda da suka buya a karkashin bishiyoyi a Borno

Sojojin sun ce sun samu nasarar ce bayan sun samu bayanan sirri game da ‘yan ta’addan.
Arewa maso gabashin Nijeriya na daga cikin wursren da 'yan ta'adda suka addaba a Nijeriya. Hoto/NAF

Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce jiragen yakinta sun kashe ‘yan ta’adda akalla 22 da suka buya a karkashin bishiyoyi a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwa da daraktan watsa labarai na sojin saman kasar Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar a ranar Litinin, ya ce sojojin sun samu nasarar ne bayan sun samu bayanan sirri kan ‘yan ta’addan.

“Bayan bayanan sirrin da aka samu daga sojojin kasa na Operation Hadin Kai a ranar 29 ga watan Oktoban 2023 cewa an hangi ‘yan ta’adda kusan 22 a cikin motar girke bindiga da babura biyu a kusa da Marte, sai nan-take aka tura sojojin sama na OPHK zuwa wurin,” in ji sanarwar.

“Bayan duba wurin, sai aka hangi ‘yan ta’addan kusan kilomita 22 a yammacin Marte inda suke tafiya arewaci ta Munguno. Bayan bin sawun ‘yan ta’addan na kusan mintuna 70, sai ‘yan ta’addan da ke cikin motar girke bindigar da babura biyu suka tsaye karkashin wasu bishiyoyi, watakila domin su kara mai da kuma guje wa idon mutane,” kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.

Daga nan ne aka bude wuta kan maboyar tasu, inda aka lalata motar girke bindigar da baburan ba tare da wasu alamu na motsi ba.

Rundunar sojin saman ta bayyana cewa idan aka yi la’akari da irin karar fashewar da aka ji, watakila wuri ne na kayan aikinsu ko kuma motar na dauke da ababen fashewa masu yawa.

Sojojin Nijeriya suna ikirarin samun nasara a kan mayakan Boko Haram da suka addabi arewa maso gabashin kasar.

Ko a kwanakin baya sai da sojojin saman kasar suka ce sun kashe ‘yan ta’adda da dama sannan sun lalata babura sama da 40 da motocin girke bindiga shida.

TRT Afrika