Robobi suna hana ruwa gudu a magudanar ruwan jihar, in ji kwamishinan muhamallin jihar:Hoto/Reuters

Gwamnatin jihar Legas ta haramta amfani da robobin takeaway wanda ake amfani da su sau daya a jihar.

Kwamishinan muhalli da albarkatun ruwan jihar, Tokumbo Wahab ne ya bayyana hakan ranar Lahadi inda ya ce nau'in robobin sun hada da robobin soso

Mai Magana da yawun ma’aikatar muhallin jihar, Kunle Adeshina, ya ambato kwamishinan yana cewa jihar ta dauki matakin ne domin yadda robobin ke lahani ga muhallin jihar inda suke toshe magudanan ruwa saboda yadda ake amfani da su ba tare da kulawa ba.

Ya ce robobin abincin ne suka fi yawa a cikin ababen da hukumar kwashe shara a jihar ke fama da su.

Adeshina ya ce jami’an hukumar yaki da rashin da’a da jami’an hukumar kwashe ta a jihar za su afka wa masu samarwa da sayar da irin wadannan robobin a fadin jihar saboda a dakile yaduwar robobin.

Wahab ya gargadi masu samarwa ko kuma sayar da robobin cewa matakin da za a dauka zai iya kai ga rufe kamfanoninsu idan ba su daina ba.

TRT Afrika