Hedkwatar ta ce sojojin ƙasar sun kashe ‘yan ta’adda 8,034 kuma suka kama mutum 11,623 da ake zargi da ta’addanci tare da kuɓutar da mutum 6,376 da aka yi garkuwa da su daga watan Janairu zuwa watan Disambar 2024.
Daraktan watsa labarai a hedkwatar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan sojin ƙasar a birnin Abuja a ranar Alhamis.
Janar Buba ya ce tun daga farkon shekarar ne dakarun suka fuskanci barazana daban-daban a wurare biyar a fadin ƙasar.
Ya ce sojojin sun kasance a shirye tsaf domin kare ƙasar daga farmaƙin 'yan ta'adda da kuma rashin tsaro.
Janar Buba ya ce sojojin sun kama makamai 8,216 da harsasai 211,459 tare da ƙwato ɗanyen mai da aka sata da ya kai kimanin naira biliyan 57 cikin watanni 11 da suka gabata.
“Makaman sun haɗa da bindigogi ƙirar AK47 4,053 da kuma bindigogi da aka ƙera a cikin gida 1,123 da baushe 731 da kuma bindgogi ƙirar pump action 240,” in ji daraktan.
Kazalika Janar Buba ya ce sojojin sun kwace harsasai da aluburusai iri-iri kimanin dubu dari biyu.
“Bugu da ƙari, dakarun sun kwace danyen mai da aka sace da ya kai lita miliyan 53.1 da kuma lita miliyan 9.1 na man gas da lita 90,595 na kananzir da lita 156,095 na man fetur da aka tace ba bisa ƙa’ida ba,” in ji daraktan.
A arewa maso gabashin ƙasar, Janar Buba ya ce dakarun Operation Hadin Kai, sun kashe ‘yan ta’adda 2,918 kuma suka kama mutum 2,285 da ake zargi da ta’addanci tare da kuɓutar da mutum 1,496 da aka yi garkuwa da su.
Ya ƙara da cewa mayaƙan Boko Haram da ISWAP da iyalansu 15,950 ne suka miƙa wuya ga sojojin Nijeriya.
“Arewa maso –tsakiyar Nijeriya dakarun Operation Safe Haven sun kashe masu tsatsauran ra’ayi 411 1,859 tare da kwato mutum 927 da aka yi garkuwa da suda kuma makamai da harshasai.
“A ƙarƙashin Operation Whirl Stroke, dakarun sun kashe ‘yan ta’adda 583 kuma suka kama mutum 916 da ake zargi da ta’addanci tare da kuɓutar da mutum 649 da aka yi garkuwa da su.
“A kudu maso –yammaci kuma dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan ta’adda 2,646 suka kuma kama mutum 1,654 da ake zargi da ta’addanci tare da ‘yanta mutum 2,339 da aka yi garkuwa da su.
“A ƙarƙshin Operation Whirl Punch, dakarun sun kashe ‘yan ta’adda 732 suka kuma kama mutum 1,842 da ake zargi da ta’addanci tare da kubutar da mutum 569 da aka yi garkuwa da su,” in ji Buba .
Ya ƙara da cewa a kudu maso gabashin ƙasar, dakarun Operation UDO KA sun kashe ‘yan ta’adda 666 kuma suka kama mutum 893 da ake zargi da ta’addanci tare da ‘yanta mutum 323 da aka yi garkuwa da su a lokacin.