Janar-Janar  da ke rikici da juna a Sudan sun ki yin sulhu

Janar-Janar  da ke rikici da juna a Sudan sun ki yin sulhu

Kwanaki shida kenan da fara rikici tsakanin dakarun sojin Sudan da mayakan RSF.
'Yan kasar ta  Sudan suna ta tserewa daga Khartoum yayin da ake cigaba da fafatawa tsakanin bangarorin biyu/ Hoto: Reuters

Rundunar sojin Sudan da dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun bayyana cewa shugabanninsu ba za su yi sulhu da juna ba don shawo kan rikicin da ke faruwa a kasar.

Rundunar sojin ta bukaci dakarun RSF su mika wuya.

"Bai kamata al'ummar Sudan su sha wahala a lokacin karamar Sallah ba, kuma son kan dakarun RSF ne ya kawo mu cikin wannan hali. Rundunar soji ta dukufa wajen kare kasar nan da kuma dawo da martabar 'ya'yanta," a cewar babban hafsan rundunar sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan a hirarsa da gidan talbijin na Al Jazeera.

Shugaban RSF Janar Mohamed Hamdan Dagalo ya tabbatar wa manema labarai cewa sun gaza cimma matsaya don tsagaita wuta.

Hakan na faruwa ne a yayin da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tattauna ta wayar tarho da shugaban rundunar sojin Sudan Al-Burhan da Kwamandan RSF Hemedti.

A sanarwar da fadar shugaban kasar Turkiyya ta fitar an bayyana cewa a ganawar tasu ta wayar tarho an tattauna halin da ake ciki a Sudan, kuma suna bibiyar dukkan abubuwan da ke faruwa a kasar.

Shugaba Erdogan ya ce “Turkiyya ta goyi bayan ayyukan mika mulki ga farar hula a Sudan.

"Mun gayyaci dukkan bangarorin da su dakatar da yaki su dawo teburin sulhu. Mun kuma yi kira ga Sudan da ta dauki matakan da suka kamata don hadin kan jama’ar kasar."

Shugaban na Turkiyya ya ci gaba da cewa “Za mu ci gaba da tsayawa da goyon bayan ‘yar uwarmu Sudan, a shirye muke mu bayar da dukkan taimakon da ake bukata.”

Erdogan ya ce sun yi kira da a dauki matakan tsagaita wuta don bude filin tashi da saukar jiragen saman Khartoum ta yadda ‘yan kasar Turkiyya da ke Sudan za su dawo gida, sannan a kuma samu damar gudanar da ayyukan jin kai.

An cigaba da musayar harbe-harben bindigogi da jin karar fashewar bama-bamai a Khartoum, babban birnin Sudan ranar Alhamis a yayin da ake arangama tsakanin bangarorin biyu.

TRT World