Shugaban mulkin sojin Nijar ya zargi Faransa da shirin "wargaza ƙasar — watanni bakwai bayan ya kori sojojin Faransa da ke yaƙi da ta'addanci daga ƙasar.
"Wannan cuta ta son wargaza Nijar ta watsu ta hanyar dasa dukkan jami'ai na hukumomin leƙen asirin Faransa (French DGSE) waɗanda muka kora daga ƙasarmu," in ji Janar Abdourahamane Tiani, a wani jawabi na awanni biyu da ya yi ta gidan talbijin na ƙasar don biki cikarta shekara 64 da samun 'yanci.
Gwamnatin Janar Tiani ta kawo sauye-sauye a dangantakarta da ƙasashen duniya tun bayan da ya jagoranci juyin mulki na ranar 26 ga watan Yulin bara.
Ya kori dukkan dakarun Faransa waɗanda aka jibge a yankin Sahel domin yaƙi da masu iƙirarin jihadi daga Nijar.
"An ajiye (dakarun Faransa a Nijeriya da Benin domin wargaza mu," in ji Janar Tiani, yana mai cewa wasu daga cikinsu suna "sanye da fararen kaya" da kuma "wasu dakarun rundunar sojojin Benin waɗanda su ma suna sanye da fararen kaya".
Sake buɗe iyaka da Benin
Jamhuriyar Nijar tana yawan zargin maƙociyarta Benin da kafa "sansanin sojojin Faransa", ko da yake hukumomin Benin da na Faransa sun sha musanta zargin.
Waɗannan zarge-zarge ne suka haifar da rashin jituwa ta diflomasiyya ta wata da watanni tsakanin Nijar da Benin, wacce ta hasala sakamakon takunkuman da ƙungiyar ECOWAS ta sanya mata bayan juyin mulkin.
Duk da yake an janye takunkuman a watan Fabrairu, mahukunta a Yamai sun ƙi buɗe iyakarsu da Benin sannan sun rufe bututun man da suke sayar wa ga ƙasashen waje da ya ratsa ta tashoshin jiragen ruwan Benin.
"Duk ranar da muka fahimci cewa ba za mu fuskanci wata barazana daga Benin ba, za mu ɗauki matakan da suka dace" na sake buɗe iyakarmu, in ji Tiani.
Yayin da Nijar take taƙaddama da Benin, a gefe guda tana yauƙaƙa dangantaka da maƙotanta Burkina Faso da Mali, waɗanda su ma sojoji ne suke mulki.
Tiani ya ce ƙungiyar da ƙasashen uku suka kafa wato Alliance of Sahel States, za ta ba su damar amfana da juna musamman ta fannin ɗanyen mai na Nijar.