Wasu Sojojin Ƙungiyar Tarayyar Turai EU a Nijar./ Hoto: AA

Jamus za ta bar sansanin sojinta da ke Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar a buɗe har zuwa wani ɗan lokaci, kamar yadda ma'aikatar tsaron ƙasar da ke Berlin ta bayyana a ranar Talata.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan sanarwar ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) kan shirin kammala aikin haɗin-gwiwa na soji wanda ya ƙunshi sojojinta da dama da suke jibge a Nijar a ranar 30 ga watan Yuni.

Berlin na da sojoji kusan 90 a birnin Yamai a halin yanzu.

Har zuwa lokacin da aka yi juyin mulki a Nijar a shekarar 2023, ƙasar na ɗaya daga cikin ƙawayen ƙungiyar Tarayyar Turai a yankin Sahel inda ake yaƙi da masu tayar da ƙayar baya da suka kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da matsugunansu.

Ko da yake, shugabannin mulkin sojin ƙasar sun yi matuƙar matsa wa Faransa wacce ta yi wa Nijar ɗin mulkin mallaka har sai da ta janye dakarunta.

Haka kuma sun yanke hulɗar soji da Amurka wadda suka bai wa umarni ta kwashe sojojinta daga ƙasar, yayin da a gefe guda suka ƙarfafa alaƙa da Rasha.

"Jamus da Nijar sun ƙulla yarjejeniyar wucin gadi da za ta ba da damar ci gaba da kasancewar sojojin Jamus a Nijar," a cewar wata sanarwa da ma'aikatar tsaron Jamus ta fitar, inda ta ƙara da cewa hakan zai bai wa Berlin damar ci gaba da buɗe sansaninta da ke ƙasar har bayan ranar 31 ga watan Mayu.

Tun a shekara ta 2013 ne Jamus take amfani da sansanin sojin da ke Yamai a matsayin cibiyar samar da kayan aiki ga dakarunta da ke maƙwabciyar ƙasar Mali inda suke aiki a cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (MINUSMA).

A ƙarshen shekarar 2023 ne dai sojojin Jamus na ƙarshe suka fice daga Mali.

Ko da ya ke ba a bayyana takamaiman shirin Berlin na ci gaba da amfani da sansanin a Yamai ba.

Ma'aikatar tsaron ta ce yarjejeniyar ta wucin gadi ta ba da damar cimma sabuwar yarjejeniyar wadda za ta ba da damar kasancewar sojojin Jamus a Nijar.

A yanzu haka dai, sojojin za su ci gaba da gudanar da ayyukansu a sansanin tare da rage yawan sojojin da suke jibge a wurin, a cewar sanarwar.

A ranar Litinin ne, ƙungiyar EU ta sanar da kawo ƙarshen aikin soji da ya ƙunshi sojoji da dama a Nijar daga yanzu har zuwa ranar 30 ga watan Yuni, tana mai kafa hujja kan ''halin da ake ciki na siyasa'' a ƙarƙashin mulkin soji a Nijar.

A shekarar 2022 ne aka soma aikin haɗin-gwiwar a ɗaya daga cikin ƙasashe mafi fama da talauci a duniya inda aka jibge dakarun sojin Turai 50 zuwa 100 don su taimaka wajen samar da tsaro da ci gaba.

AFP