Hukumar zaɓen Kano da ke arewacin Nijeriya (KANSIEC) ta sanar da 'yan takarar jam'iyyar NNPP mai mulkin Jihar a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen duka shugabannin ƙananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar.
Jam'iyyar ta NNPP ta cinye zaɓukan ƙananan hukumomi 44 da na kansiloli 484, a cewar shugaban hukumar zaɓe na jihar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi.
"Kamar yadda duniya ta gani, an yi wannan zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana tare da cikakkaiyar samun nasara...bisa ga sakamakon da wakilan hukumar zaɓe na ƙananan hukumomi suka miƙo mana, jam'iyyar NNPP ta lashe duka kujerun shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli 484," in ji Farfesa Malumfashi.
Ya ƙara da cewa jam'iyyu shida ne suka fafata a zaɓen.
Jam’iyyun su ne: Nigeria People Party (NNPP), Zenith Labour Party (ZLP) Accord Party (AP) National Rescue Movement (NRM), African Action Congress (AAC) da Action Alliance (AA).
Babbar jam’iyyar adawa a Jihar, APC, ta ƙaurace wa zaɓen.
Zaɓen dai ya fuskanci ƙalubale daban-daban domin kuwa Kotun Tarayyar Nijeriya ta haramta gudanar da shi bayan da ta ce wasu mambobin hukumar zaɓen ta Kano, ciki har da shugabanta Farfesa Malumfashi, 'ya‘yan Jam’iyyar NNPP ne.
Sai dai kotun jihar Kano ta yi hukunci wanda ya ci karo da na tarayya inda ita kuma ta umarci hukumar zaɓen ta Kano da ta gudanar da zaɓen a ranar Asabar.
Ita kuwa rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta bi umarnin kotu, inda ta ƙaurace wa zaɓen.
Amma jami’an hukumar Hisbah da ‘yan Karota sun tabbatar da tsaro a rumfunan zaɓe.