Jam'iyyar ANC ta Afirka ta Kudu ta cim ma yarjejeniyar ƙawance da jam'iyyar DA

Jam'iyyar ANC ta Afirka ta Kudu ta cim ma yarjejeniyar ƙawance da jam'iyyar DA

Jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu ta cim ma yarjejeniyar haɗaka da jam'iyyar Democratic Allience.
Jam'iyyar ANC ta Shugaba Cyril Ramaphosa na neman a sake zaɓarta. / Hoto: AP

Jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu ta ƙulla yarjejeniyar ƙawance da jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance (DA).

Kafar yaɗa labaran ƙasar ta SABC ta rawaito a ranar Juma'a cewa yarjejeniyar wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ANC ke yi na kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa, wanda ke nufin raba madafun iko.

Yarjejeniyar ta zamo abar farin ciki ga magoya bayan ANC, waɗanda ke fatan shugaba Cyril Ramaphosa ya sake samun wa'adin shugabancin ƙasar.

Majalisar dokokin Afrika ta Kudu za ta kaɗa kuri’ar zaɓen shugaban ƙasa ranar Juma’a.

Yawancin 'yan majalisa sun sha kaye

ANC ta samu kujeru 159 na majalisar dokoki, yayin da DA ta samu kujeru 87 a zaɓen da aka gudanar a ranar 29 ga watan Mayu.

Idan aka haɗa kuri'unsu za su zarce 201 da ake buƙata don lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Zaɓen na baya-bayan nan shi ne karo na farko da ANC ta gaza samun aƙalla kashi 50% na ƙuri’un ‘yan majalisa tun 1994.

Wasu daga fitattun jam'iyyun da har yanzu ba su bayyana matsayin tattaunawarsu da ANC ba, sun haɗa da Economic Freedom Fighters (EFF) da Inkatha Freedom Party (IFP).

Jam'iyyar tsohon Shugaban Ƙasa Jacob Zuma uMkhonto weSizwe, wadda ta samu kujeru 58 na 'yan majalisar dokoki a zaɓukan da aka gudanar a baya-bayan nan, ta yi watsi da buƙatar kiran da ANC ta yi na a yi haɗaka.

Ƙananan jam'iyyun siyasa a Afirka ta Kudu na da ƙuri'u 57 a majalisar dokokin ƙasar.

TRT Afrika