Faure Gnassingbe, shugaban jam'iyya mai mulki a Togo ya kasance a kan kujerar shugaban kasa tun shekarar 2005. / Hoto: AA

Jam'iyya mai mulki a Togo ta yi nasara da babban rinjaye a zaben yankuna da aka gudanar a watan da ya gabata, in ji hukumar zaben kasar a wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin.

Hakan na nufin nasara ga Shugaba Faure Gnassingbe, wanda ya samu rinjaye a zaben 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a baya.

An yi zaben 'yan majalisar dokoki da na kansilolin yankuna a ranar 29 ga Afrilu bayan kwaskwarima ga kundin tsarin mulki wanda 'yan adawa suka ce ya bai wa Gnassingbe ikon ƙarfafa mulkin da danginsa ke yi na kusan shekaru 60 a kasar.

Jam'iyyar Hadin Kan Jumhuriya ta Gnassingbe ta lashe kujerun kansilolin yankuna 137 daga cikin 179, kamar yadda sakamakon da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta fitar a ranar Litinin ya nuna.

Jam'iyyun adawa da 'yan takara masu zaman kansu sun lashe kujerun kansiloli 39.

Kwaskwarima ga Kundin Tsarin Mulki

Dole sai bangaren shari'a na kasar ya amince da zabukan guda biyu - sannan kotun kundin tsarin mulki ta sake amince wa da zaben 'yan majalisar dokoki, haka ma Kotun Koli za ta amince da zabukan yankuna.

An gudanar da zabukan bayan kwaskwarima ga kundin tsarin mulki da ya sauya kasar Togo daga mai amfani da tsarin shugaban kasa zuwa tsarin firaminista, matakin da 'yan adawar kasar ta Yammacin Affirka suka kira a matsayin 'juyin mulki a hukumance'.

A ranar Litinin, Gnassingbe ya bayar da umarnin karshe na sanya hannu kan sabon kundin tsarin mulki, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta bayyana.

A karkashin sabon kundin tsarin mulkin, ofishin shugaban kasa zai zama na je ka na yi ka, kuma 'yan majalisa ne za su dinga zabar wanda zai zama shugaban kasa.

Gnassingbe na iya hawa babban matsayi

A yanzu karfin ikon zartarwa zai zama a hannun Shugaban Majalisar Ministoci, kamar dai firaminista da zai zama shugaban jam'iyya da ke da rinjaye a majalisar dokoki.

Hakan na nufin Gnassingbe na iya zama sabon shugaban jam'iyyarsa ta UNIR. A karkashin tsohon kundin tsarin mulki, yana da karin zangon mulki daya ne zuwa 2025.

A 2005 ne sojoji suka kakaba Gnassingbe a kan mulkin Togo bayan rasuwar mahaifinsa a 2005, kuma tuni ya yi nasara a zabukan kasar hudu da aka gudanar a tsawon kusan shekaru 40.

'Yan adawa na tsammanin Gnassingbe ya rike sabon mukamin har nan da shekara shida, matukar jam'iyyarsa na da rinjaye a majalisa.

'Nuƙu-Nuƙun Zabe'

Sabbin kansilolin da aka zaba za su kasance daga cikin wadanda za su zabi majalisar dattawa da aka kirkira karkashin tsarin gudanarwa mai firaminista da magoya bayan UNIR suke cewa ya sake daga darajar dimokuradiyyar Togo.

'Yan adawa a Togo na cewa suna buƙatar sake gyara jam'iyyunsu bayan sun lashe kujeru biyar kacal daga 113 na majalisar kasa, wanda suka ce an yi musu 'muna-munar zabe' ne.

Masu sanya idanu daga Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS da Tarayyar Afirka da Kungiyar Kasa da Kasa ta La Francaphone sun bayyana gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin.

TRT Afrika