A watan jiya, an kashe 'yan ƙasar China huɗu a wani wurin haƙar ma'adinai a harin da aka zargi Coalition of Patriots for Change da kaiwa./Hoto: Reuters Archive

Gwamnatin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ta dakatar da wani kamfanin China da ke haƙar ma'adinai daga aiki a ƙasar, inda ta zarge shi da haɗa baki da ƙungiyoyin 'yan bindiga, a cewar wata sanarwa da gwamnati ta fitar.

Ma'aikatar harkoki ma'adinai ta ƙasar ta zargi kamfanin Daqing SARL na ƙasar China da ke haƙar zinare da azurfa da "haɗa baki da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, da tatsar bayai da kuma kawo wasu abubuwa daga waje wurin da ake haƙar ma'adinai da rashin biyan haraji da ƙin bayar da bayanai game da ayyukan da yake yi."

Kamfanin Daqing SARL yana gudanar da ayyukansa a garin Mingala da ke kudancin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, inda dakarun gwamnati suke gwabza faɗa da gamayyar ƙungiyoyin masu riƙe da makamai mai suna Coalition of Patriots for Change.

Kamfanonin China ne suka fi gudanar da harkokin haƙar ma'adinai a ƙasar ko da yake suna fuskantar matsalar rashin tsaro.

A watan jiya, an kashe 'yan ƙasar China huɗu a wani wurin haƙar ma'adinai a harin da aka zargi Coalition of Patriots for Change da kaiwa.

Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ta tsunduna cikin rikici tun shekarar 2013, lokacin da 'yan tawaye suka ƙwace mulki daga hannun Shugaba Francois Bozize.

Wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanya wa hannu a shekarar 2019 ba ta sa an daina rikicin ba, kuma ƙungiyoyi shida daga cikin 14 na masu riƙe da makamai da suka shiga yarjejeniyar sun fice daga cikinsa daga bisani.

An kafa ƙungiyar Coalition of Patriots for Change a shekara 2020 bayan ƙulla yarjejeniyar.

AP