Ouattara, wanda aka sake zaɓarsa a shekarar 2022, har yanzu bai bayyana ko zai sake tsayawa takarar ta gaba ba. / Photo: AA

Shugaban ƙasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya cire firaminista tare da rusa majalisar gwamnatin kasar, kamar yadda sakataren fadar shugaban kasa Aboudramane Cisse ya faɗa a ranar Juma'a.

Ba a faɗi dalilin ɗaukar matakin ba.

"Shugaban ƙasa yana miƙa godiyarsa ga Firaminista Patrick Achi da dukkan mambobin gwamnatinsa kan jajircewarsu da hidimar da suka yi wa ƙasar a tsawon shekaru," in ji Cisse.

Za su ci gaba da zama a muƙamansu na ɗan lokaci har sai an naɗa sabon firaminista da ƴan majalisar gwamnati, ya ƙara da cewa.

Ba a saba ganin shugabannin ƙasa suna ɗaukar irin waɗannan tsauraran matakan ba a Ivory Coast, da kuma yi wa gwamnatocinsu garanbawul.

A watan Afrilun bara ne Achi ya miƙa takardarsa ta barin aiki da ta mambobin gwamnatinsa bayan da Ouattara ya sanar da shirye-shiryensa na rage yawan ministocin gwamnatin.

Mako guda bayan nan ne aka sake zaɓar firaministan.

A shekarar 2025 ne za a gudanar da zaɓe a Ivory Coast. Ouattara, wanda aka sake zaɓarsa a shekarar 2022, har yanzu bai bayyana ko zai sake tsayawa takarar ta gaba ba.

Reuters