Libya / Photo: AP

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iraki ta bayyana cewa za ta sake bude ofishin jakadanci a Libiya shekara tara bayan rufe shi saboda dalilan tsaro.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Irakin, Ahmed Al-Sahhaf ya ce “Iraki ta yanke hukuncin sake bude ofishin jakadancinta a Libiya tare da dawo da ayyukan diflomasiyya don karfafa alakar kasashen biyu.

Wannan sanarwa ta zo ne makonni uku bayan da Iraki ta bayyana bukatar sake bude ofishin jakadancin nata a Tarabulus.

A ranar 16 ga Maris Al-Sahhaf ya ce an dauki wannan mataki ne a yayin tattaunawar wakilan gwamnatocin Iraki da Libiya.

Bangaren Libiya bai ce komai ba game da wannan batu.

Kasashen duniya da yawa da suka hada da Iraki sun rufe ofisoshin jakadancinsu a Libiya a 2014 lokacin da rikici ya tsananta a kasar.

AA