Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umarni ga jami'an tsaro su zaƙulo mutanen da suka kashe sojojin ƙasar da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar Abia da ke kudu maso gabashin ƙasar.
Ya bayar da umarnin ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar da maraice inda ya yi alhinin kisan sojoji biyar da ake zargi mayaƙan ƙungiyar IPOB da ke neman ɓallewa daga Nijeriya sun yi a birnin Aba ranar 30 ga watan Mayu.
" 'Yan ta'adda na ƙungiyar IPOB/ ESN ne suka kai hari sannan suka kashe dakarunmu na Rundunar OP UDO KA da aka tura wuraren binciken ababen hawa na Obikabia a ƙaramar hukumar Obingwa da ke maƙwabtaka da birnin Aba na jihar Abia," in ji wata sanarwa da rundunar sojojin Nijeriya ta fitar ranar Juma'a.
Lamarin ya faru ne a ranar da masu fafutukar a-ware na Biafra suke juyayi na shekara-shekara kan yaƙin Biafra wanda aka soma ranar 30 ga watan Mayun 1967.
Shugaba Tinubu ya ce, "Na samu baƙin-labari na kisan sojoji biyar da ake zargin ƙungiyar ta'addaci ta IPOB da aka haramta ta yi. Sojojin da aka kashe suna aikin wanzar da zaman lafiya a Aba, jihar Abia, ranar Alhamis yayin da aka kashe su, watanni biyu bayan aukuwar irin wannan lamari a Okuama na jihar Delta".
Shugaban na Nijeriya ya yi Allah wadarai da kisan wanda ya bayyana a matsayin "dabbanci" kuma "aikin shaiɗanu" da ba za a taɓa amince da shi ba.
Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayyar Nijeriya da rundunar sojojin ƙasar suna da ƙarfin murƙushe duk wasu masu neman tayar da tarzoma da haddasa rashin zaman lafiya.
"Ina kira ga jami'an tsaro su zaƙulo waɗanda suka kitsa kai hari a Abba da kuma waɗanda suke kira mutane su zauna a gida. Abin da suke yi ba komai ba ne face cin amanar ƙasar," in ji Shugaba Tinubu.
Kazalika ya yi ta'aziyya ga iyalan sojojin da aka kashe da rundunar sojojin Nijeriya, yana mai kira ga jami'an tsaro da kada su karaya wajen aikin wanzar da tsaro a ƙasar.