Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin lalacewar wayoyin ba. / Hoto: AP

An samu matsalar ɗaukewar intanet a wasu sassan yankunan Yammacin Afirka da Tsakiyar Afirka sakamakon lalacewar wayoyin da suke ƙarƙashin gaɓr tekun Afirka daga yammaci.

Aƙalla wayoyi uku ne na ƙarƙashin tekun suka lalace a ranar Alhamis, kamar yadda wani kamfani mai sa ido kan harkokin intanet, Netblocks ya faɗa, yana mai cewa kamfanonin intanet da yawa sun ba da rahoton afkuwar matsalar.

Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin lalacewar wayoyin ba.

Kamfanin da ke kula da wayoyin inatent na ƙarƙashin teku na Afirka SEACOM ya tabbatar da cewa ayyukan intanet sun katse a Afirka kuma dole ta sa abokan cinikin da suka dogara da su suka koma kan amfani da wayoyin inatent na Google Equiano na ɗan lokaci.

Alkaluma na Netblocks sun nuna cewa lamarin ya fi shafar ƙasar Ivory Coast sosai, sai kuma ƙasashen Laberiya da Benin da Ghana da Burkina Faso.

Sannan wani kamfanin inatnet na Cloudflare a shafinsa na X ya ce an kuma samu matsalar intanet ɗin a Gambia da Guinea da Liberia da Ghana da kuma Nijar.

TRT Afrika da abokan hulda