Sauran ɓangarorin da rahoton ya ƙunsa sun haɗa da batun kai kayan zaɓe, da batun tsaro, da ɗaukar ma’aikata da kuma ba su horo. Hoto: INEC X

Hukumar zaben Nijeriya mai zaman kanta INEC ta fitar da rahoto kan zaben shekarar 2023, wanda a ciki ta yi bayani dalla-dalla kan duk wasu batutuwa da suka shafi zaɓen.

Rahoton mai shafi 526 da babi 13, ya yi cikakken bayani kan hanyoyin da aka bi wajen gudanar da zaɓen, da nasarori da matsalolin da aka samu, da kuma darussan da aka koya.

Wata sanarwa da Kwamishina mai kula da watsa labarai da wayar da kai, Sam Olumekun ya fitar a ranar Juma’a, ta ce an fitar da rahoton a matakin hukumar na yin komai ƙeƙe-da-ƙeƙe.

INEC ta fitar da wannan rahoto ne kusan shekara guda bayan yin manyan zaɓukan Nijeriya, wanda a ƙarshe sai da aka dangana kotu da wasu daga ciki, inda wasu jam’iyyun da ba su yi nasara ba suka ƙalubalanta.

Rahoton ya yi bayani dalla-dalla kan damuwar da jama’a suka nuna kan nau’rar tura sakamakon zabe iRev, inda INEC ta yi bayani kan matsalolin da aka fuskanta wajen tura sakamakon zaɓen shugaban kasa.

Haka kuma rahoton ya yi nuni kan irin yadda aka yi amfani da kimiyya wajen inganta zaɓen, musamman ma amfani da na’urar BVAS wajen tantance masu zaɓe, abin da rahoton ya ce hakan ya taimaka wajen ƙara wa zaɓen Nijeriya martaba da kuma rage cuwa-cuwa.

“Sauran ɓangarorin da rahoton ya ƙunsa sun haɗa da batun kai kayan zaɓe, da batun tsaro, da ɗaukar ma’aikata da kuma ba su horo,” a cewar Sam Olumekun.

Kazalika, rahoton ya kuma yi nuni da yadda aka samu bambance-bambancen da ba a taɓa gani ba a zaɓen na wakilcin jam’iyyu, wanda ke nuna gagarumin ci gaban dimokuradiyya.

“Jam’iyyun siyasa huɗu ne suka yi nasara a zaɓen gwamnoni, sai jam’iyyu bakwai a kujerun sanatoci, da takwas a mazaɓar majalisar tarayya da kuma jam’iyyu tara a tsakanin ‘yan majalisun jihohi, lamarin da ke nuni da gagarumin sauyi na wakilcin siyasa a faɗin Nijeriya,” in ji sanarwar.

INEC ta nemi yan Nijeriya da su aike mata da martaninsu a kan abin da rahoton ya ƙunsa ta yadda za ta sanya su a cikin sauye-sauye inganta zaɓen a nan gaba.

TRT Afrika